Wata tawagar Fastoci dake karkashin wata kungiyar mabiya addinin Kirista ta 'United for Change Association', ta roki gwamnatin Nij...
Wata tawagar
Fastoci dake karkashin wata kungiyar mabiya addinin Kirista ta 'United for
Change Association', ta roki gwamnatin Nijeriya da kuma rundunonin sojin kasar
da su kaddamar da gagarumin farmaki kan ‘yan bindigar da suka addabi mutane, ta
hanyar yi musu ruwan bama-bamai a cikin dazukan da suke boye a yankunan arewa
maso yammaci, jihar Neja da kuma sauran yankin arewa ta tsakiya.
Limaman Cocin
sun kuma roki shugaban Nijeriya Muhammad Buhari da ya yi amfani da matsayinsa
na Babban Kwamandan daukacin rundunonin tsaron kasar, ya ba da umarnin fara
amfani da sabbin jiragen yaki na zamani kirar Super Tucano da gwamnatinsa ta
sayo daga Turai, domin murkushe ‘yan ta’addan kowa ma ya huta.
Shugaban
kungiyar Fastocin David Adeniran ne ya yi wannan kira, yayin taron nemana
labarai da ya gudanar a garin Kaduna, inda ya yi kira da al’ummar Musulmi da ma
Kiristoci da su yi amfani da lokacin watan Ramadan wajen yawaita addu’o’in
neman samun zaman lafiya.
Karuwar
ta’addancin na 'yan bindiga da ake fuskanta a baya bayan nan ne ya sanya
gwamnonin wasu daga cikin jihohin arewacin Nijeriya, suka ce a shirye suke su
nemo sojin haya domin kare rayuka da kuma dukiyoyin al’umma, matukar dai matsalar
ta ci gaba da ta’azzara.
Gwamnan jihar
Kaduna Nasir El-rufai, wanda ya zanta da wakilin RFI Hausa, Muhammad Kabiru
Yusuf bayan da ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari a cikin makon da ya
gabata, inda ya ce babban abin takaici shi ne yadda jami’an tsaro suka gaza
daukar matakin murkushe ‘yan bindigar duk da cewa ana da cikakkun bayanai a
game da maboyarsu.
No comments