Mataimakin Gwamnan Katsina, Mannir Yakubu Ya Ajiye Muƙaminsa Na Kwamishinan Aikin Gona


Mataimakin Gwamnan jihar Katsina,  Mannir Yakubu Ya Yi murabus daga mukamin sa na Kwamishinan ayyukan gona.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da mai taimaka masa ta fanni Yaɗa Labarai Malam Ibrahim Musa Kalla ya sanya wa hannu aka raba wa manema labarai a Katsina.

Sanarwa ta kara da cewa Mataimakin Gwamna, Alhaji Mannir Yakubu ajiye aikinsa na Kwamishinan Aikin Gona domin bin sabuwar dokar Zaɓe da kuma neman Kujerar Gwamnan Jihar Katsina.

Post a Comment

0 Comments