Uwargidan shugaban Nijeriya Aisha Muhammadu Buhari ta wallafa wani sako a shafinta na Facebook inda a ciki ta yi wa al'ummar...
Uwargidan shugaban Nijeriya Aisha Muhammadu Buhari ta wallafa wani sako a shafinta na Facebook inda a ciki ta yi wa al'ummar jihar Zamfara ta arewa maso yammacin najeriya addu'ar zaman lafiya.
Aisha Buhari ta wallafa sakon ne da misalin karfe 12:09 na daren Laraba, inda ta roki Allah ya samar wa mutanen jihar mafita daga matsalar tsaron da ta addabe ta, musamman a wannan daren da Musulmi ke raya dare domin neman falalar Lailatul Kadri:
"Allah ya fitar da mu da mutanen jihar Zamfara daga chikin wannan hali, albarkacin daren Lailatul Kadri, Ameen!"
Baya ga sakon, uwargidan shugaban Najeriyar ta kuma wallafa wani sako na sauti mai tsawon minti 3:53, wanda a ciki ana iya jin wani mutumin da bai fadi sunansa ba yana sanar da wani mutumin da ya kira 'Haji Abdurrahman' labarin wani kamun da 'yan sa-kai suka yi wa wasu barayin daji a yankin Tsafe da Mada na jihar Zamfara.
A farkon sautin ana iya jin muryar wata mata da ke cewa, "Ga shi ku ji me yake fada..." Sai dai ba mu san ko muryar ta uwargidan shugaba Buhari ba ce.
No comments