Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Matsalar Tsaro Ta Fi Karfin Buhari, Inji Obasanjo

  Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a jiya ya bayyana rashin tsaro da ke addabar kasar a matsayin 'babbar matsala', kuma ya...

 


Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a jiya ya bayyana rashin tsaro da ke addabar kasar a matsayin 'babbar matsala', kuma ya ce ya kamata masu ruwa da tsaki su hada karfi da karfe domin magance matsalar.

Tsohon shugaban ya furta kalaman ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library da ke Abeokuta a jihar Ogun, yayin da yake karbar Dakta Ugochukwu Williams, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP da tawagarsa.

Tsohon shugaban ya ce matsalar tsaron ta gagari gwamnatin Muhammadu Buhari. "Idan wani ya zo nan ya ce ina son ganinka, zan amsa ma sa da cewa gani, saboda halin da muke ciki a Najeriya yafi karfin wani mutum daya ya ce yana da mafita. Na yi imanin sai mun zauna tare kuma mun duba al'amarin tare."

Jaridar Vanguard ta Najeriya ta ruwaito shi yana cewa, "Cikin wannan halin babu wanda ke da cikakken tsaro ko a kan hanyar mota, ko a cikin jirgin kasa, ko ma a filin jirgin sama. Lalali akwai babbar matsala."

"Ya kamata dukkan 'yan Najeriya su sani cewa mun fda cikin wata matsalar da ta gagari gwamnati mai-ci, amma bai kamata mu bari matsalar ta fi karfin Najeriya ba, inji shi".No comments