Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mutane 100 Sun Mutu A Wani Haramtaccen Wurin Tace Danyen Mai A Nijeriya

Rfi Hausa ta labarto cewa; ana fargabar cewar akalla mutane sama da 100 suka mutu sakamakon wata gobarar da ta tashi a wajen tac...


Rfi Hausa ta labarto cewa; ana fargabar cewar akalla mutane sama da 100 suka mutu sakamakon wata gobarar da ta tashi a wajen tace danyan man fetur ba bisa ka’ida ba akan iyakokin Jihohin Imo da Rivers da ke Nijeriya.

Jaridar Vanguard da ake wallafawa a Najeriyar tace shugaban wata Cibiyar manufofin matasa da muhalli da ake kira ‘Youth and Environment Advocacy Centre’, Fyneface Dumnamene ne ya shaida mata labarin hadarin wanda yace ya faru a Abacheka dake karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni a Jihar Rivers.

Sai dai mai magana da yawun ‘Yan Sandan Jihar Rivers Grace Iringe-Koko tace yankin ba a cikin Jihar Rivers yake ba, inda ta kara da cewar yana Jihar Imo ne.

Jaridar tace Fyneface wanda ya gabatar mata da wasu hotunan hadarin da babu kyaun gani, yace bayan mutanen da suka kone kurmus, wasu motocin da suke dakon a zuba musu man satar suma sun kone kurmus.

Ko a makon jiya sanda aka samu irin wannan hadari a karamar hukumar Rumuekpe Emohua inda mutane sama ad 30 suka mutu cikin su harda yara, abinda gwamnatin Jihar Rivers ta danganta shi da fashewaer gas da satar man.

Jihohin Rivers da Imo na daga cikin wadanda ke fama da matsalar fasa bututun mai ana sata da kuma masu tace man a haramtattun matata.

A farkon shekarar nan Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya kaddamar da samame akan barayin man da zummar dakile ayyukan su saboda abinda ya kira zagon kasa da matakin nasu ke yiwa tattalin arzikin Nijeriya.

No comments