Jam'iyar APC na binciken yadda Naira miliyan 44.2 suka yi batan dabo ranar Laraba a sakatariyar jam'iyar da ke Abuja. Ba...
Jam'iyar APC na binciken yadda Naira miliyan 44.2 suka yi batan dabo ranar Laraba a sakatariyar jam'iyar da ke Abuja.
Batan kudin ya janyo dakatar da sayar da fom din 'yan takara, musamman 'yan takarar da ke son tsayawa takarar mukaman 'yan majalisar wakilai da na dattawa.
Jam'iyyar ta kafa wasu rumfuna domin sayar da fom din ga masu son tsayawa takara.
Sai dai da misalin karfe 4:15, jam'iyyar ta cire rumfunan kuma ta umarci ma'aikatanta su ci gaba da sayar da fom din a cibiyar gudanar da taruka ta International Conference Centre da ke Abuja.
Jaridar Daily Post ta ce wannan matakin ya biyo bayan bacewar dalar Amurka 75,000 ne wanda yayi daidai da Naira miliyan 44.2.
Wani ma'aikacin jamiyyar da baya son a bayyana sunansa ya ce an cire rumfunan ne bayan da aka gane kudaden sun yi batan dabo.
Ma'aikacin ya ce "Mun ji cewa wani mutum da yazo sakatariyar jam'iyyar, sai dai saboda yawan jama'a bai iya shiga cikin ginin ba da motarsa. Amma yayin da yake kokarin shiga cikin ginin, mun ji wai wani ambulan da yake dauke da shi wanda dala 75,000 ke ciki ya fadi."
No comments