Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ni Takarar Shugaban Ƙasa Zan Tsaya -Wike

 Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, mai neman takarar shugaban kasa, ya ce ba zai yarda da a bashi toshiyar bakin takarar mataim...



 Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, mai neman takarar shugaban kasa, ya ce ba zai yarda da a bashi toshiyar bakin takarar mataimakin shugaban kasa ba.

"Ban fito don  don na sasanta da wani na zame masa mataimaki a takara ba. Ni na fito ne domin in tsaya takarar shugaban ƙasa," in ji Wike, wanda ya shaida wa shugabannin jam'iyyar a Benin a jiya Alhamis.

Aike ya koka da yadda yanayin rashin tsaro ya mamaye kasar, yana mai cewa akwai bukatar Nijeriya ta kashe makudan kudade wajen tattara bayanan sirri domin dakile taɓarɓarewar tsaro.

Gwamnan na PDP ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ke haddasa rashin tsaro da ake fama da shi a kasar nan shi ne gazawar Gwamnatin Tarayya wajen kashe isassun kudade domin tattara bayanan sirri kan dakile matsalar tsaro.

“Akwai bukatar kashe isassun kudade wajen nemo da bayanan sirri don dakile rashin tsaro a kasar. Ba ku jira don ƙyale abubuwan da suka faru su faru ba kafin ƙoƙarin magance su. "

Wike ya bayyana cewa, ka’idojin farko da kowane shugaban kasa zai yi nasara a Najeriya shi ne yadda irin wannan shugaban zai iya tabbatar da tsaron kasa da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

No comments