Wani binciken masana ya bayyana cewar Nijeriya ce kasa ta 3 da aka fi cin naman kare a duniya, bayan kasashen Koriya ta Kudu da Vietnam. ...
Wani binciken masana ya
bayyana cewar Nijeriya ce kasa ta 3 da aka fi cin naman kare a duniya, bayan
kasashen Koriya ta Kudu da Vietnam.
Rahotan binciken da
Mathew Nash ya jagoranta wanda Jaridar Premium Times ta wallafa yayi karin
haske akan kasashen da kiwon karnuka ke da tasiri da akasin haka a wannan
shekara ta 2022.
Rahotan ya ce duk da ya
ke ana matukar cin naman karan lokacin bukukuwa a China, kasar bata cikin jerin
kasashe 3 na duniya da akafi cin naman karan kamar yadda binciken da aka
gudanar a kasashe 51 ya nuna.
Wannan binciken ya
mayar da hankali ne akan kasashen da ake kare hakkin karnukan da kasashen da
ake barin karnukan su shiga otel-otel da wadanda ke da isassun likitocin dake
kula da su da masu kungiyoyin kare hakin dabbobi da masu fama da barazanar
kamuwa da cutar cizon karnukan da kuma wadanda ke da dokar alaka tsakanin
dabbobi da mutane.
Nijeriya ta zo ta 45
daga kasashe 51 da suka cika mizanin binciken da aka gudanar da maki 44.41,
yayin da Italia ke matsayi na farko sai New Zealand sannan Faransa da Birtaniya
da Jamus.
Duk da matsayin Nijeriya
na zama kasa ta 3 da aka fi cin naman karen, a watan Yulin bara akalla mutane
18,000 suka sanya hannu akan wata takardar korafi inda suka bukaci shugaban
kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin sa da su haramta cin naman karen da kuma
sayar da shi.
Naman karen dai yana da
matsayi sosai a wasu jihohin kudancin Nijeriya da suka hada da Akwa Ibom da
Cross Rivers da kuma Rivers inda aka masa lakabi da 404.
No comments