Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Nijeriya Ta Fi Kowacce Kasa Fama Da Zazzabin Cizon Sauro A Duniya

Ministan Lafiyar Nijeriya Dakta Osagie Ehanire, ya ce kasar tafi kowacce kasa yawan masu kamuwa da zazzabin cizon sauro ko Malar...


Ministan Lafiyar Nijeriya Dakta Osagie Ehanire, ya ce kasar tafi kowacce kasa yawan masu kamuwa da zazzabin cizon sauro ko Malaria da kuma mace-macen da cutar ke haddasawa.

Ministan ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya gabata ranar Laraba a Abuja, yayin taron tunawa da ranar zazzabin cizon sauro ta duniya a karkashin jagorancin ma’aikatar lafiyar Najeriya tare da hadin gwiwar kungiyar masu fafutukar dakile cutar zazzabin na cizon sauro ta 'Roll Back Malaria' suka shirya da sauran masu ruwa da tsaki.

Da yake tsokaci kan rahoton zazzabin cizon sauro na duniya na shekarar 2021, ya ce kashi 27 cikin 100 na yawan wadanda ke kamuwa da zazzabin Malaria a Najeriya suke, zalika kasar ke da kashi 27 cikin 100 na yawan wadanda cutar ke kashewa a duniya.

Wata kididdiga ta daban kuma ta nuna cewar, cutar ta Malria na shafar akalla kashi 98 cikin 100 na al’ummar Najeriya, kamar yadda karamin Ministan Lafiya a kasar Olorunimbe Mamora ya tabbatar.

No comments