A yau Litinin Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zabei 2023. “A yau, ...
A yau Litinin Mataimakin
shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar
shugaban kasa a zabei 2023.
“A yau, cikin
tawali’u, a hukumance na bayyana aniyara ta tsayawa takarar shugaban kasar Tarayyar
Najeriya a Babbar jam’iyyarmu ta APC,” in ji shi a wani faifan bidiyo da ya
wallafa a shafinsa na Facebook.
Sanarwar na sa
ta kawo karshen cece-kucen da aka yi na tsawon watanni a kan sha’awarsa a
takarar shugaban kasa a 2023 tare da fadada tarin ‘yan takarar kujerar a APC
wanda ya hada da Bola Ahmed Tinubu, Rotimi Amaechi, Dave Umahi, Yahaya Bello.
Hakan kuma ya
sanya shi yin arangama kai tsaye da tsohon Ubangidansa a jihar Legas, Bola
Ahmed Tinubu, wanda ya nuna aniyarsa a farkon shekarar.
A cikin
jawabinsa na tsawo minti shida da dakikoki, Fasto Osinbajo ya ce zai jajirce
wajen ci gaba da manufofin shugaban kasa Muhammadu Buhari ga kasar.
“Da yardar Allah
da yardar jama’a idan aka ba ni dama, to na yi imanin cewa da farko, dole ne mu
kammala abin da muka faro, tare da sauya fasalin tsarin tsaro da leken asiri,”
in ji shi.
No comments