Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

PDP Ta Haramtawa Ƴan Takara Biyu Yin Takarar Shugaban Ƙasa

Rahotanni sun ce babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta hana wa biyu daga cikin 'yan takarar shugaban kasa 17 a zaben 2023 yi...


Rahotanni sun ce babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta hana wa biyu daga cikin 'yan takarar shugaban kasa 17 a zaben 2023 yin takara ƙarƙashin jam’iyyar.

Jaridar Premium Times da ta ruwaito labarin ta ce shugaban kwamitin tantance ƴan takarar David Mark, bai bayyana sunayen waɗanda aka hana wa yin takarar ba da kuma dalilin rashin cancantarsu.

Daga cikin ƴan takarar da aka tantance a ranar Juma’a a hedikwatar jam’iyyar a Abuja sun ƙunshi tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar da tsohon shugaban Majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan Kwara Sanata Bukola Saraki da gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da gwamnan Bauchi Bala Muhammad da Peter Obi da Pius Anyim.

No comments