Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ramadan: Abdulaziz Yari Ya Gwangwaje Mutanen Zamfara Da Abincin Azumi

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari Abubakar, ya bada tallafin kayan abincin Azumi kimanin tirela dari da saba’in ga a...Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari Abubakar, ya bada tallafin kayan abincin Azumi kimanin tirela dari da saba’in ga al’ummar Jihar Zamfara domin saukaka musu dawainiyar Azumi.

Motoci dauke da abincin Azumi da Abdulaziz Yari ya raba a Zamfara. 

Kayan abincin da tsohon gwamnan ya rabar sun hada da Shinkafi Tirela 50, Gero Tilera 50, Masara Tilera 50 da Sukari shi kuma tilera 22 da za a rabar ga mabukata a fadin jihar a cikin wannan watan na Ramadana.

Sanata Kabiru Marafa wanda ya wakilci tsohon gwamnan wajen kaddamar da rabon kayan abincin, shi ne ya bayyana haka a lokacin kaddamar da bada kayan a Gusau babban Birnin Jihar Zamfara a ranar Juma’a.

Marafa ya bayyana cewa, tsahon gwamnan Abdulaziz Yari, ya saba a kowace shekara yana bada tallafin kayan abincin Azumi ga al’ummar Jihar Zamfara, “Amma a wannan shekarar tsahon gwamnam ya ninka fiye da na shekarun da suka gabata, domin a bana tirela dari da saba’in da biyu za a raba na kayan abincin.”

Sanata Marafa ya kara da cewa, wadanda za su amfana da tallafin abincin sun kunshi ‘yan Siyasa da ‘yan gudun hijira da marayu, kuma an sanya kwamiti mai karfi da zai kula da raba kayan don tabbatar da an yi adalci wajen wannan rabon ga mabukata da marasa karfi a cikin al’umma.

A karshe Sanata Marafa, ya jinjina wa tsahon gwamna Yari akan yadda har zuwa yanzu al’umar jihar suna ransa duk kuwa da cewa baya gwamnati a halin yanzu, sai ya masa addu’ar fatan alkairi.

A nasa jawabin babban Kwamandan yakin neman zaben Yari, Alhaji Nabature Nahuce, ya nuna farin cikinsa da al’umar jihar da suka rabauta da irin wannan dimbin kayan abincin ta hannun tsohon gwamnan a cikin irin wannan lokacin da ake kokarin shiga watan Azumi.

Kuma wannan ya tabbatar mana da cewa, yana tare da al’umar Jihar Zamfara, suma suna tare da shi jiki da tsako duk tsanani duk Wuya.

Yari ya nuna mana karara har zuwa yanzu al’uma Jihar Zamfara suna zuciyarsa, Yari shi ma yana tare da su dari bisa dari.

No comments