Wata Ƙungiya mai Zaman Kanta, mai suna Al-Mubarak Waqf Foundation ta raba Naira Miliyan 2 da su U ɗari 9 a matsayin Zakka ga wani masallac...
Wata Ƙungiya mai
Zaman Kanta, mai suna Al-Mubarak Waqf Foundation ta raba Naira Miliyan 2 da su
U ɗari 9 a matsayin Zakka ga wani masallaci, gidan marayu da wasu ɗaiɗaikun
al'umma a Jihar Kano.
Da ya ke jawabi
a yayin rabon zakkar, jami'i a ƙungiyar, Dakta Jamilu Chedi, ya ce an zaɓi waɗanda
su ka amfana da zakkar ne duba da dacewar su.
A cewar Chedi,
ƙungiyar na da burin ta faɗaɗa wadanda za ta riƙa baiwa zakkar da ga shekara
mai zuwa.
Ya ƙara da cewa
ƙungiyar, wacce a ka ƙafa ta a 2019, an samar da ita ne domin taimaka wa
al'umma da kuma bunƙasa ilimi ga ƴan uwa Musulmi, inda ya ƙara da cewa za ta
riƙa tallafa wa wajen ci gaban fasahar zamani da sana'o'i a cikin al'ummar
Musulmi.
Dakta Chedi ya
kuma baiyana cewa a yanzu haka kungiyar na gina masaallacin Juma'a a unguwar
Na'ibawa da ke Jihar Kano, inda ya ƙara da cewa su na kokarin ganin an taimaka
wa masu ƙaramin ƙarfi a cikin al'umma don samun zaman lafiya.
Da ya ke jawabi
a madadin wadanda su ka amfana da zakkar, Junaidu Ahmad ya nuna jin daɗi da
godiya ga ƙungiyar, inda ya tabbatar mata da cewa za su yi amfani da kuɗin da a
ka basu ta hanyar da ta dace.
No comments