Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da ke shan suka kan kin yin tir da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, ya caccaki kwamitin su...
Shugaban
kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da ke shan suka kan kin yin tir da mamayar
da Rasha ta yi wa Ukraine, ya caccaki kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya
da cewa ya na bukatar garambawul don tafiya dai dai da zamanin da ake.
Shugaban
Cyril Ramaphosa ya ce rikici tsakanin Rasha da Ukraine ya fallasa gazawar da
kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke da shi wajen gudanar da ayyukansa
don tabbatar da zaman lafiya a sassan Duniya.
A
cewar shugaban wanda har zuwa yanzu kasar sa ta ki yin tir da Rasha haka zalika
ta kauracewa kada kuri'a a kudurorin majalisar 2 da aka amince da su kan
Ukraine, ya zargi mahukuntan kasashe da zamowa 'yan amshin shata, yana mai cewa
babu hadin kai a lamurran tabbatar da zaman lafiya ga sassan duniya daga zauren
Majalisar.
Ramaphosa
wanda ke bayyana hakan ga manema labarai a birnin Pretoria, ya ce tsarin na
Majalisar Dinkin Duniya ya bai wa kasashe masu karfi damar yin amfani da
karfinsu wajen yanke shawarwarin da a wasu lokuta su ke da hadari, lamarin da a
cewarsa irin wadannan tsare-tsare sun tsufa da halin da duniya ke ciki a yanzu.
Shugaban
na Afrika ta kudu kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika, ya
ce akwai bukatar dawo da tsarin Demokradiyya a zauren Majalisar ta yadda
majalisar za ta kasance mai gaskiya ga aikinta da kuma kaucewa wuce gona da iri
da wasu tsirarun kasashe ke yi.
Wannan
kalamai na Ramaphosa na zuwa ne a dai dai lokacin da a yau Alhamis Majalisar
Dinkin Duniya ta kada kuri'ar da ta dakatar da Rasha daga kasancewa mamba a
kwamitin kare hakkin dan adam na Majalisar sakamakon abin da ta ke aikatawa a
Ukraine, hukuncin da ke biyo bayan bukatar hakan daga Amurka.
No comments