Karim Benzema ya taimakawa Real Madrid matsowa ga lashe lashe gasar La Liga na Spaine bayan doke Sevilla da ci 3 – 2. Masu masaukin baki w...
Karim Benzema ya taimakawa Real Madrid matsowa ga lashe lashe gasar La Liga na Spaine bayan doke Sevilla da ci 3 – 2.
Masu masaukin baki wato Sevilla suka fara zura kwalaye har biyu a ragar Real Madrid ta hannun ‘yan wasanta Ivan Rakitic da kuma Erik Lamela a mintuna 21 da 26 da soma wasa kuma har aka tafi hutun rabin lokaci a haka.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Madrid ta fara farke kwallon farko a mintuna na 50 ta hannun Rodrygo, sai a mintuna na 82 Nacho ya farke akayi canjaras, 2 -2 kafin daga bisani Benzema ya kara kwallo na uku ana daf da tashi wasa.
Da wannan sakamako Real Madrid ta baiwa masu biye da ita ratan maki 15 a saman teburin La Liga, duk da cewa har yanzu akwai sauran wasannin shida.
Sevilla, da ta sha kayi ta ci gaba da kasancewa a mataki na uku da uku a saman teburi da maki 60 daidai da Barcelona dake mataki na biyu da kuma Atletico Madrid a matsayi na hudu.
No comments