Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rikici Ya Barke Tsakanin Naziru Da Nafisa A Goman Ƙarshe Na Ramadan

*Babu wanda iyayensa suka haifa suka rasa yadda za su yi da shi sama da macen da za ta dunga kama otel tana iskanci tana turawa ...


*Babu wanda iyayensa suka haifa suka rasa yadda za su yi da shi sama da macen da za ta dunga kama otel tana iskanci tana turawa duniya - Naziru Sarkin Waƙa

Mawaki Naziru sarkin waka ya yi hannunka mai sanda ga abokiyar sana’arsa Nafisa Abdullahi bayan ta kalubalanci Almajiranci.

Sarkin Waka ya ce babu wanda iyayensa suka haife sa suka rasa yadda za su yi da shi sama da macen da za ta dunga kama otel tana iskanci tana turawa duniya.

Ya ce abun da ya fi bashi haushi shi ne a ce mutumin da ba zai iya karanta Fatiha yadda take ba amma yana zagin almajirai da wasun su sun rubuta Al-Qur’ani.

Shahararren mawaki, Naziru Sarkin waka ya sake yin zazzafan martani a kan furucin da jaruma Nafisa Abdullahi ta yi kan Almajirai da iyayensu.

Sarkin waka ya nuna bacin ransa, inda ya bayyana cewa babu wanda iyayensa suka yi asarar haihuwarsa sama da mutumin da zai dunga iskanci yana sakin hotuna duniya na zaginsa amma shi ko a jikinsa.

Mawakin ya kara da cewar wasu daga cikin masu martanin ma ko cikakkiyar Fatiha ba za su iya kawowa ba amma suke zagin almajirai wanda a cikinsu harda wanda ya rubuta Al-Kur’ani.

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a a shafinsa na Instagram, Naziru ya kuma ce wadanda iyayensa suka yi asarar haihuwarsa ita ce wacce za ta tafi uwa duniya ta kama otel tana abubuwan da ta ga dama.

Ya ce: "Tsari da jama’a idan zan yi magana ko idan na yi magana sai a ce bana son zaman lafiya, ba haka bane ba. Idan dai zaka fadi gaskiya ne ake fadar haka amma idan zaka fadi wani abu makamancin haka ba haka bane, kuma bana fada don wani ya ji haushi, ban taba fada domin in ta da hazo ba, ban kuma fada don wani ya dubi shafina ba babu abun da ya shafe ni da wannan ni kodayaushe fejina a cikin godiyar Allah take.

"Akwai wanda iyayensa suka haife shi ba su san yadda za su yi da shi ba ya wuce mutumin da haka kawai zai tashi ya tafi chan, in mace ce ta je ta kame gida ko otel kullum tana otel", inji shi. 

No comments