‘Yan bindigar da suka kai hari kan jirgin kasan dake zirga zirga tsakanin Abuja zuwa Kadunan Najeriya sun karbi diyyar naira miliyan 100 k...
‘Yan
bindigar da suka kai hari kan jirgin kasan dake zirga zirga tsakanin Abuja zuwa
Kadunan Najeriya sun karbi diyyar naira miliyan 100 kafin sakin shugaban bankin
kula da ayyukan noma na kasar Alwan Hassan bayan ya kwashe kwanaki kusan 10 a
hannunsu.
Jaridar
Daily Nigerian da ake wallafawa a kasar tace sabanin faifan bidiyon da ‘Yan
bindigar suka gabatar cewar sun saki Hassan ne saboda yawan shekarun sa da kuma
azumin watan Ramadan, wata majiya kusa da iyalan sa ta tabbatar da cewar sanda
suka karbi makudan kudin kafin sakin sa.
Jaridar
ta ce ‘Yan bindigar sun aike da sakon bidiyo ga iyalan Manajan Bankin inda suka
bukaci a kaimu musu kudin ko kuma su hallaka shi, abinda ya sa iyalan suka kai
musu kudin a wani dajin Jihar Kaduna, domin kubutar da shi.
Majiyar
ta shaidawa Jaridar cewar da farko an umurci iyalan da su kai kudin wani daji
dake Jihar Katsina, amma kuma daga bisani sai akace musu su koma Jihar Kaduna,
inda suka cimma tarin ‘Yan bindigar dauke da makamai a wani daji, suka kuma
mika musu makudan kudin.
'Yan bindiga sun yi ikirarin rashin karbar kudin fansa
Faifan
bidiyon da ‘Yan bindigar suka gabatar na nuna cewar su basu karbi ko kwabo ba
daga hannun Manajan bankin kuma sun sake shi ne saboda yawan shekarunsa, inda
suka bukaci gwamnatin Najeriya da ta biya musu bukatun su ko kuma su hallaka
tarin fasinjojin dake hannun su yanzu haka.
‘Yan
bindigar wadanda suka rufe fuskokin su a bidiyon da suka gabatar dauke da
manyan bindigogi, sun ce ita gwamnati ta san bukatun su, saboda haka suna
jiranta, kuma idan ta gaza zasu hallaka fasinjojin da suka kama.
Hukumar kula da sufurin jiragen
kasa a Najeriya tace akalla fasinjoji sama da 140 ba’a iya ganin su ba bayan
kazamin harin da aka kaiwa jirgin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 28
ga watan Maris, yayin da wasu majiyoyi ke cewa wadanda suka bata sun zarce
wannan adadi ganin yawan mutanen dake neman ‘yan uwan su da suka bata.
No comments