Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shaikh Zakzaky Ya Aikawa Da Ƴan Gudun Hijira A Sakkwato Tallafin Kayan Abinci

Daga Bilal Nasir Umar Sakkwato Da yammacin jiya Juma'a 28 ga watan Ramadan shekara ta 1443 daidai da 29 ga watan Afrilun shekara ta ...


Daga Bilal Nasir Umar Sakkwato

Da yammacin jiya Juma'a 28 ga watan Ramadan shekara ta 1443 daidai da 29 ga watan Afrilun shekara ta 2022 saƙon tallafin kayan abinci da Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya aiko ga ƴan gudun hijira na garin Gandi dake cikin ƙaramar hukumar Raɓah ta jihar Sakkwato ya isa a hannunsu. Tallafin kayan abincin da suka haɗa da Shinkafa, Taliya, Indomie, Madara, da sauran su. 

Malam Sidi Munir waƙilin ƴan'uwa musulmi almajiran Shaikh Zakzaky na Sakkwato ne ya jagoranci kai kayan ga ƴan gudun hijirar da suka fito daga garuruwa daban-daban waɗanda hare-haren ƴan ta'adda ya shafa.

An kuma miƙa kayan ne ga Malam Bello Amadu wanda shi ne yake kula da sansanin ƴan gudun hijira dake garin na Gandi, haka kuma an rarraba kayan ga Hakimai na kowanne gari inda shi kuma Hakimi zai sadar da kayan ga jama'arsa.

Daga cikin garuruwan da ƴan gudun hijirar suka fito akwai; Taɓanni, Alikkiyo, Rakwamni, Ruwan Tsamiya, Tafkin Kwasa, da sauran su. 

Jama'a sun yi godiya matuƙa tare da jin daɗi na wannan gudummuwar da suka samu tare da yin addu'o'i na musamman ga jagoran Harkar Musulunci Shaikh Zakzaky.

Ga wasu hotunan raba tallafin; 

No comments