Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Shaikh Zakzaky Ya Ce Al'amarin Kudus Na Duk Musulmi Ne

Wannan shi ne cikakken jawabin da Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi a yau Laraba 26 ga watan Ramadan 1...


Wannan shi ne cikakken jawabin da Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi a yau Laraba 26 ga watan Ramadan 1443 daidai da 27 ga watan Afrilun 2022 wanda Gidan Talabijin na ABS CHANNEL TV suka wallafa a shafinsu na YouTube. Ammar M. Rajab ya rubuta muku.

Bismillahir Rahmanir Rahim. Wasallallahu Ala Sayyidina Wa Nabiyyina Muhammadin Wa’alihid Dahirin.

Assalamu Alaikum warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu.

GABATARWA KAN GOYON BAYA GA AL’UMMAR FALASDINU

Yau Laraba a lissafinmu daidai da ashirin da shida ga watan Ramadan hijira dubu da dari hudu da arba’in da uku (26 ga watan Ramadan 1443).  To a daidai wannan lokaci da muke a Ramadan; tun farawar Ramadan din nan za ka ga cewa ainihin abin da ke faruwa a birni mai tsarki; birnin Kudus na kullum ana ta kai hare-hare a kan al’ummar Musulmi na Falasdinu da suke sallah a Masjidul Aksa da kuma yadda ake ta kai musu hare-hare har a gidajen kwanansu. Da kullum yaumin sai ka ji tun bayan kamawar Ramadan din nan haramtacciyar kasar Isra’ila sai kai hare-hare suke ta ta yi a al’ummar Falasdinu suna ta kisa. To wannan ya jawo fushin al’ummar Musulmi da ma al’ummar duniya baki daya a wurare daban-daban ana ta fitowa ana muzaharori da nuna Allah-wadai da nuna irin wannan ta’asa da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi a kan al’ummar Falasdinu.

Na ga wani irin taro mai yawan gaske wanda aka yi a Bangaladesh wanda mutane suka fito da yawan gaske, kuma har wala yau an nuna a kasashen Turai ma a Jamani da Ingila harda Amerika; duk mutane sun fiffito suna ta nuna damuwa akan abin da ake yi ma al’ummar Falasdinu. Don haka tun ma kafin ranar Kudus ainihin ana ta wadannan muzaharori saboda haka bai kamata mu ma a nan bangare a bar mu a baya ba; yakamata wannan al’ummar da muke zaune a ciki su ma duniya ta san cewa akwai masu kokawa, ba wai sai ranar Kudus ba wanda zai zo jibi (Juma’a). Harma a yau Larabar nan da kuma ma gobe Alhamis da bayan ma Kudus din duk lokaci ne na nuna tadamuni da al’ummar Falasdin ta hanyoyi daban-daban za a nuna ana tare da Falasdinu. Daya daga cikinsu shi ne daga tutar ainihin Falasdinu da kuma rubuce-rubuce a kafafen sadarwa na sada zumunta daban-daban wanda idan mutum ya duba zai ga akwai wadansu kiraye-kiraye da ake yi. Kamar abin da ake ce ma ‘Fly Palestinian Flag’ idan ka sa #FlyPalastinianflag za ka ga ainihin rubuce-rubuce daban-daban da hotuna daban-daban a wurare daban-daban ana ta daga tutocin falasdinu don nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu.

WANNAN KUDUS DIN YAKAMATA YA ZAMA NA MUSAMMAN

To wannan Kudus din ainihin na wannan karon yakamata ya zama na musamman. Musamman cewa mu shekara takwas da suka wuce ainihin ranar Kudus ta dace da ranar 28 ga watan Ramadan kuma ranar nan ainihin an bude wuta akan ainihin ‘yan’uwa a Zariya wanda aka kashe mutum 34. Saboda haka wannan lokaci ma ne ya dace da duk ranar 28 akan yi jajen shahadar wadannan shahidai wanda da yawansu an bizne su a Darur Rahma ne, idan banda kadan daga ciki. Cikin 34 din nan muna iya cewa kamar 31 ainihin an bizne su ne a Darur Rahma. Saboda haka ya kan kasance duk ranar 28 akan tuna da su wadannan shuhada din a daga hotunan shahidai din. Kuma mu tuna ma mutane abin da ya faru a Zariya a wancan lokaci a daidai wannan lokacin kudus din. Da kuma ma ranekun Kudus da suka gabata wanda wadannan mutane suka ga su ya dace su a wurinsu a nan su bude mana wuta ne. Saboda haka ranar wannan Kudus din zai zama a lokaci guda lokacin tunawa da abin da ya faru shekara takwas da suka wuce a ranar Kudus a Zariya.

Har wala yau kuma daidai wannan lokaci kamar yadda nake cewa ba ranar Kudus din kawai ba ranar Juma’a ba, harma sauran raneku saboda abin da ke faruwa a Falasdinu a halin yanzu. Yakamata muzaharori ya zama kulli yaumin ko da wanne lokaci ainihin ana nuna tadamun da al’ummar Falasdinu ta hanyoyi daban-daban da kuma yin addu’o’i a lokacin addu’o’inmu daban-daban.

TUNATARWA KAN DAREN 27 GA WATAN RAMADAN

To kuma na sha tunatar da ‘yan’uwa a rana mai kamar ta yau a lokacin da muke tafsiri; ranar 26 ga wata mu kan ce to gabanmu fa ga wani dare mai muhimmanci daren 27 ga Ramadan wanda ainihin da yawan al’ummar Musulmi sukan dauka ma shi ne Lailatul Kadr. Tunda ainihin Laylatul Kadr bisa hikimar Allah ta’ala an boye ba a ce dare ayyananne kamar kaza bane. Saboda haka da yawansu akan nemi daren ne a goman karshe na Ramadan; a goman karshen ma a daren mara, a maran ma akan fi fifita wadansu darare. To da yawan Musulmi suna fifita daren 27. Harma za ka ga masallatai sun cika ranar nan saboda ana tunanin ranar ne mai yiwuwa ta zama Laylatul Kadr wanda Allah ta’ala ya ce; ‘ta fi dare dubu’.

Mu a wajenmu akwai dararen da muke ce musu Layalil Kadr; muna fifita su da ruwayoyi daban-daban akan cewa su wadannan daya daga cikinsu shi ne Laylatul Kadr, amma kuma duka wadannan dararen gaba dayansu suma ana ce musu Layalil Kadr ba Laylatul Kadr kwara daya bane. Suma Layalil Kadr ne, saboda mene? Duk abin da za a zartar a daren Laylatul Kadr, to ana shisshiryawa a tantance su a wadannan darare; daren karshe ya zama an zartar. Saboda haka na sha tunatar da ‘yan’uwa a lokaci mai kama da wannan cewa ka da ya zama wanda suke ganin daren 27 a matsayin Laylatul Kadr su zo su fi ka. Kar ka dauka don ka raya Layalil Kadr din da suka gabata ka yi sake a daren 27; ka da wani wanda shi ba yana mazhabanka bane ya zama ya fika ibadodi a wanann dare din. Saboda haka ya yi maka karin kaimin ibada.

An samu ruwaya cewa Imam Zainul Abidin (AS) an ji shi a daren 27 tun farkon daren har karshen daren yana yawaita addu’a yana cewa; ‘Allahumar zukni tajafiya an darir gurur wal iynaabata ila Daril khulud wal isti’idadal mauti kabla khululul fauti’.

اللَّهُمَّ ٱرْزُقْنِي ٱلتَّجَافِيَ عَنْ دَارِ ٱلْغُرُوروَٱلإِنَابَةَ إِلَىٰ دَارِ ٱلْخُلُودِوَٱلاِسْتِعدَادَ ِلْمَوْتِ قَبْلَ حُلُولِ ٱلْفَوتِ

 

Mutum ya dunga maimaita shi; ‘Allahumar zukni tajafiya an darir gurur wal iynaabata ila Daril khulud wal isti’idadal mauti kabla khululul fauti’. Ma’ana ainihin kana rokon Allah ka azurta ni da nisantar gidan rudu wato duniya ke nan da kuma karkata ya zuwa gidan dawwama; lahira ke nan. Da kuma tanadin mutuwa kafin kubucewar lokaci; wato kafin ainihin kubucewa ya sauka. Wato ma’ana ainihin kubucewar lokaci ya zama mutuwa ta zo ba ka shirya ba.

Wato kana rokon Allah ta’ala; Allah ya azurtaka nisantar gidan rudu; wannan duniyar ke nan wanda ba ta dawwama da kuma karkata ya zuwa gidan dawwama; lahira ke nan wanda nan zamu je mu dawwama dindindin; da kuma tanadin mutuwa kafin kurewar lokaci. Don idan mutuwa ta zo ba ka shirya ba shi ke nan ba jiranka za ta yi ba.

To kuma a cikin wani dogon addu’a na Imam Zainul Abideen wanda yake yi a daidai rana mai kamar ta yau yana cewa; Allahummar zukni alafata anil duniya..; Allah ka azurta ni da kyamar duniya, domin ainihin sabonta yana tsufa, mai dadinta yana lalacewa, ainihin mai kamshinta kan koma ya zama wari sannan danyenta yana zuwa ya rube, mulkinta na gushewa, da sauran su da sauran su cewa komai na ta mai gushewa ne ainihin bai kamata ya zama kai wannan kake hankoro ba. Ko ma ka yi hankoron duniya; duniyar za ta zo ta kubuce maka. Dukiya kake da, ko mulki kake da, ko mene ne ma ita duniya tana kubucewa, amma gobe kiyama idan an je zaman dindindin ne. Allah ya taimake mu baki daya.

Wasallallahu Ala Muhammad Wa’alihid Dayyibinad Dahirin. Wassalamu alaikum warahmatullah ta’ala wabarakatuhu.


DAUKAR NAUYIN KAWO CIKAKKEN BAYANIN: Dandalin Yada Labarai Na Harkar Musulunci Na Yankin Zariya ne suka ɗauki nauyin kawo muku wannan labarin. 

No comments