Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Shari'ar Isa Ashiru: Alƙali Ya Sanya Ranar Yanke Hukunci

Daga Umar Idris Honorabul Justice Kabiru Dabo na Babbar kotu mai lamba 1, Dogarawa, Zariya a karamar hukumar Sabon Gari da ke ji...


Daga Umar Idris

Honorabul Justice Kabiru Dabo na Babbar kotu mai lamba 1, Dogarawa, Zariya a karamar hukumar Sabon Gari da ke jihar Kaduna ya tsayar da ranar 27 ga watan Afirilun 2022 domin yanke hukunci na karshe a kan ikirarin rashin mafi karancin mataki na ilimi da tsarin mulki ya tanadar domin yin takarar gwamna a jihar Kaduna. 

A wannan shari'a, Abdullahi Isa ne ya shigar da karar Honorabul Ashiru Mohammad Isa.  A yayin da masu kare wanda ake kara ke duba karar da aka shigar ta hanyar tambayar wanda ya shigar da kara, Samuel Atung SAN, ya ce ya shigar da karar ne sakamakon tunanin abin da ka iya zuwa ya komo sakamakon bayanan da Mainan Zazzau, Sani Bello, ya yi. 

Sashen shari'ar masu kare Ashiru sun tambayi mai karar ko ya taba yin rubutu zuwa ga hukumar zabe ta kasa wato INEC ko kuma zuwa ga dukkanin makarantun da wanda ya shigar kara ya ce ya yi domin tabbatar da takardun makarantar wanda ya ke kara (Honorabul Ashiru) ya ce yana da su, sai wanda ya shigar da karar ya amsa da "A'a."

Wanda ya shigar da karar sai ya ci gaba da cewa ya shigar da karar ne domin tsoron da ya ke ji a matsayinsa na memba a jam'iyyar PDP cewa idan Honorabul Ashiru ya yi takara kuma ya ci a zabe mai zuwa ana iya tsayar da nasarar da ya samu a kotun sauraron kararrakin zabe. 

Honorabul Isa Mohammed Ashiru a cikin shaidar da ya gabatar ya nuna takardun kammala karatu guda shida da makarantu daban-daban suka ba shi ciki harda digiri na biyu a sashen Public Policy and Administration daga jami'ar Bayero da ke Kano.

No comments