Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Buhari Ya Yafewa Tsoffin Gwamnonin Filato Da Taraba Kan Handame Kuɗin Al'umma

Manjo Janar Buhari ya yafewa Jolly Nyame, da Joshua Dariye, tsoffin gwamnonin jihar Taraba da Filato duk da kotun koli ta same s...Manjo Janar Buhari ya yafewa Jolly Nyame, da Joshua Dariye, tsoffin gwamnonin jihar Taraba da Filato duk da kotun koli ta same su da laifin sace kuɗin 'yan ƙasa. 

Kotun farko ta sami Joshua Dariye da rubda ciki da naira Bilyan 1.162 daga kuɗin al'umma, inda ta aike shi gidan yari na shekaru 14. Sai dai kotun daukaka kara ta rage masa hukuncin zuwa shekaru 10 wanda kuma kotun koli a ƙarshe ta tabbatar da Hukuncin. 

Kazalika shima Rabaran Jolly Nyame kotu ta same shi da handame kuɗin al'umma har naira biliyan N1.6 daga asusun gwamnatin jihar, inda ta aika shi gidan yari har na shekaru 12, hukuncin da kotun koli ta tabbatar. 

Joshua Dariye da Nyame duk sun yi gwamna a jihohinsu ne daga shekarar 1999 zuwa 2007. 

Majalisar ƙasa ce dai a karkashin shugabancin, Manjo Janar Buhari (mai ritaya) ta yafewa tsoffin gwamnonin kamar yadda ministan shari'a, Abubakar Malami ya tabbatarwa da 'yan jarida a jiya Alhamis a birnin Tarayya Abuja. 

Malami ya ce cikin mutum 162 da aka nemi a yafe musu bisa Hukuncin da kotu ta yanke musu, mutum 159 ne kawai aka yarda a yafe musu. 

Malami ya ce majalisar ta ki amincewa ta yafewa daya daga cikin fursunonin da aka yankewa Hukuncin shekaru 120 bisa satar naira biliyan 25 kan cewa yana fama da matsalar rashin lafiya kamar yadda Jaridar PUNCH ta labarto.

No comments