Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Shugaban Majalisar Jihar Bauchi Ya Koma PDP Daga APC

Shugaban Majalisar Jihar Bauchi, Abubakar Suleiman ya fice da ga jami'ar APC zuwa PDP mai mulki a jihar. A wasiƙar fice wa d...


Shugaban Majalisar Jihar Bauchi, Abubakar Suleiman ya fice da ga jami'ar APC zuwa PDP mai mulki a jihar.

A wasiƙar fice wa daga APC da ya aike wa shugaban jam'iyar na mazaɓar Guda, a Ƙaramar Hukumar Ningi, Suleiman ya ce ya bar jami'ar ne sabo da rarrabuwa da ta yi a ko wanne mataki a jihar.

A cewar sa, APC ta tsatsage zuwa ɓangare-ɓangare a jihar, inda ya ƙara da cewa ko wanne ɓangare na neman cewa shi ne sahihi.

Ya ƙara da cewa shari'o'i da su ka dabaibaye jam'iyar APC a Bauchi, wanda hakan ya sanya kotu ta bada umarni ga ko wanne ɓangare sanya daina iƙirarin shugabancin jam'iyar, hakan ya sanya ya kasa gane wanne ɓangare ne mai sahihi shugabanci.

Shugaban majalisar ya ƙara da cewa matsin da ya shiga a hannun wasu a jam'iyar shi da magoya bayan sa tun da a ka zaɓe shi a matsayin Shugaba a 2019 ya sanya ya ji cewa Gara ya fice da ga jam'iyar ya yar da ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda.

Da ga ƙarshe dai ya godewa jam'iyar a bisa damar da ta bashi ya yi wa mazaɓar sa da kuma jihar hidima.

Rahotanni sun baiyana cewa tuni dai shugaban majalisar ya yanki katin jam'iyar PDP a mazaɓar ta sa ta Guda a Ƙaramar Hukumar Ningi, inda ya yi alƙawarin zai yi aiki tuƙuru wajen nasarar jam'iyar a jihar.

No comments