Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojan Nijeriya Ya Kashe Kansa Bayan Ya Shiga Hannu Kan Tuhumar Taimaka Wa ISWAP

BBC Hausa ta labarto cewa;  Rahotanni daga yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani sojan kasar ya kashe kansa bayan da ...BBC Hausa ta labarto cewa; Rahotanni daga yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani sojan kasar ya kashe kansa bayan da aka kama shi bisa zargin aiki tare da mayaka masu ikirari jihadi na kungiyar ISWAP.

Wakilin BBC ya ce wata majiya mai kusanci da rundunar sojojin Najeriya ta sanar da shi cewa lallai sojan na da hannu a wasu hare-hare da aka kai kan wasu al'umomin jihar Yobe a cikin makonni da suka gabata.

Manyan hafsoshin sojin kasar sun fara sa ido kan sojan ne bayan da aka kai wasu hare-hare biyu a garuruwan Geidam da Gashua na jihar ta Yobe, kuma daga nan suka fara bibiyar wuraren da yake zuwa cikin sirri.

An kuma kama shi yayin da yake kokarin tserewa, bayan da ya gane cewa dubunsa ta cika.

Sai dai sojan - wanda kwararre ne wajen sarrafa makamai - ya kwace wata bindiga a hannun daya daga cikin sojojin da ke rakiyarsa kuma ya kashe kansa duk da cewa an saka masa ankwa a hannu.

A makon jiya wasu wadanda ake zargi mayakan ISWAP ne suka kai wani hari kuma suka kashe akalla mutum goma, ciki har da mata.

Wannan harin ya biyo bayan wani harin na daban da aka dasa wani bam wanda ya halaka mutum shida baya ga raunata wasu mutum 19 a jihar Taraba, harin da kungiyar ISWAP ta dauki alhakin kai shi.

No comments