Sojin Ruwan Nijeriya Sun Dakile Safarar Haramtattun Kayayyaki A Neja Delta

 


Rundunar sojin ruwan Nijeriya ta kama wasu mutane da dama tare da haramtattun kayayyakin da suke safarar su, wadanda darajar kudinsu ta kai sama da dalar Amurka 700,000.

Sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Najeriyar ya fitar Comodore Adedotun Ayo-Vaughan ta ce rundunar ta ta musamman mai suna ‘Operation Dakatar Da Barawo’ wato ‘OPDDB’ ce ta samu nasarar kamen miyagun da kuma haratattun kayayyakin da suke safara, a yankunan da ake hako mai na Najeriya.

Tun a ranar 1 ga watan Afrilun nan aka kaddamar da rundunar ta ‘Operation Dakatar da Barawo’ don dakile mummunar satar albarkatun man da ake kuntukawa Najeriya.

A cikin watan Maris hukumar kula da harkokin man fetur ta Nijeriya, ta ce kasar ta yi asarar fiye da dala biliyan 3 na mai, wanda aka sace cikin watanni 14 da suka gabata.

Post a Comment

0 Comments