Karamin ministan albarkatun man fetur, kuma tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipri Marlin Sylva, ya bayar da gudunmuwar Naira mil...
Karamin ministan albarkatun man fetur, kuma tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipri Marlin Sylva, ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 5 ga shugaban darikar Tijjaniyya ta Nguru a jihar Yobe, Sheikh Muhammad Alfathi Gibrima, biyo bayan rushewar masallaci da ya yi kwanakin baya wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu da dama.
Da yake karbar tallafin, Sheikh Gibrima ya nuna jin daɗinsa ga ministan bisa wannan karamcin da ya yi musu, inda ya ce ko a matsayinsa na Kirista kuma daga kudancin kasar, ya nuna ruhin hadin kai da mutuntaka don sauran ‘yan Najeriya su yi koyi da su.
Ya kuma godewa ministan bisa kyautatawa tare da tallafawa ba tare da la'akari da bambancin addini ba.
“A madadina da kuma sauran ƴan uwana dake nan da kuma waɗanda wannan rugujewar masallacin ya shafa, ina mika godiyarmu kan tallafin kudi da muka samu daga karamin ministan albarkatun man fetur Timipri Marlin Sylva.
“Hakika wannan abun koyi ne ga sauran Kirista wanda shi ma ya fito daga Kudancin Najeriya ya kuma tallafa wa Musulmai, saboda haka yana da kyau bama kirista kawai ba hatta Musulmai muyi koyi dashi domin tallafa wa junanmu.
"Za mu ci gaba da yi masa addu'a tare da yi masa fatan alheri a duk tsawon rayuwarsa, mun yaba da wannan karimcin kuma muna godiya sosai, Allah ne kadai zai iya saka masa," in ji Sheikh Gibrima.
A lokacin da yake miƙa tallafin, wata babbar tawaga karkashin jagorancin Shugaban Jaridun Dillaliya, Kaduna, Alhaji Ibrahim Gamawa, ya bayyana karamcin da fitaccen dan siyasar ya yi a matsayin mutum mai hankali da ke fatan alheri ga kowa da kowa ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.
“Ministan Albarkatun Man Fetur Timipri Sylva yana mika muku wannan tallafin naira miliyan 5 biyo bayan wani mummunan lamari na rugujewar masallacin da ya yi sanadin mutuwar mutane tare da jikkata wasu da dama.
“Yana so in jajanta wa waɗanda suka rasa rayukansu da kuma yin addu’ar samun sauki ga waɗanda suka jikkata.
“A matsayinsa na mutum mai Rajin Kare Haƙƙin ɗan Adam, ya bayyana lamarin a matsayin abun baƙin ciki, matukar bakin ciki kuma ya cancanci irin wannan taimako daga gare shi.
“Don haka da zuciya daya ya bayar da wannan gudummawar ga shugaban yana mai bayyana sakon hadin kai da fahimtar juna a tsakanin al’ummarmu ‘yan Najeriya,” in ji jagoran tawagar.
No comments