Daga Al-Amin Ciroma Duk da wannan batu na gaban kotu, ba zai yiwu mu shiga cikin maganar gadan-gadan ba, amma dai ba laifi ba ne...
Daga Al-Amin Ciroma
Duk da wannan batu na gaban kotu, ba zai yiwu mu shiga cikin maganar gadan-gadan ba, amma dai ba laifi ba ne, a yi wa al’umma, musamman Kanawa bayanai domin su fahimci inda aka dos aba.
A ranar Laraban nan ne, hankalinmu ya kai ga wasu wallafe - Wallafe a Kafafen sada Zumunta dangane da Hukuncin da Kotun Daukaka Kara da ke Kano, ta yi a kan wata tsohuwar Shari'a ta shekarar 2020, da baban Kotun tarayya Dake Kano ta zartar, wadda ta wanke Jigo kuma dan takarar Gwamnan Jihar Kano, a karkashin jam'iyyar APC, Mai Girma, Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura, wanda aka fi sani da A. A. Zaura.
Bai zama wajibi sai an takarkare wajen mayar da bayanai ga al'umma a kan hunkuncin na Kotun ba, amma saboda kiraye-kirayen masoya, 'yan'uwa da abokan arziki, wadanda suka san gaskiyar zancen, muka ga ya zame mana wajibi, mu fito da komai fili, saboda magance yadda ake neman siyasantar da lamarin da kuma amfani da salon Farfaganda, wanda in aka bar su, za su taba mutunci da kimar dan takaran da ya fi ko wanne farin jini a cikin jam'iyyar APC a Jihar Kano.
Waiwaye dai, aka ce adon tafiya ne. A karshen shekarar 2018, lokacin da ake shirye-shiryen zabukan shekarar 2019, an kirkiri wasu kagaggun labarai, marasa tushe ballantana makama ga dan takarar Gwamnan Jihar Kano a Karkashin Jam'iyar GPN a wancan Lokacin, A. A. Zaura, inda hukumar EFCC ta ce ya taba yaudarar wani dan tahaliki, dan kasar Kuwaiti, wani wanda bai ma taba saninsa ba, balle ya san inda aka samo sunansa, Sheikh Jamal Al-Azmi kan zunzurutun kudi har Dala Milyan 1.32.
A dalilin wannan zargin ne aka gurfanar da shi a Baban Kotun tarayya Dake Kano, inda aka ce karar ta kunshi laifuka guda Tara na wai huldar kasuwanci tsakaninsa da Sheikh Al-Azmi din.
A saboda wannan dalilai ne A. A. Zaura ya yi ta jigilar zuwa Kano daga duk inda yake a duniya a lokacin, domin halartar zaman Kotun da aka rika yi, wanda tun da aka fara Shari'a kullum sai da ya zo.
Bai taba fashi ba, sai so daya, a ranar 9 ga Yunin 2020, da za a yanke hukunci, shi ma saboda dokar hana zirga-zirga da aka sa, dalilin barkewar annobar Cutar Corona. Duk da bai samu zuwa daga Abuja zuwa Kano a ranar ba, lauyansa ya halarci zaman karshen, kuma ya sanar da Kotu dalilin rashin zuwansa, Kuma Kotu ta gamsu da hakan.
A karshe, Kotun ta wanke shi daga wadannan zarge-zargen da ba su da tushe ballantana makama.
A yayin zartar da hukuncin, Alkalin Kotun, Mai Shari'a, Lewis Allagoa a hukuncisa ya ce:
"Dukkanin zarge-zargen da hukumar EFCC ta gabatar a kan Abdulsalam Zaura, ba su da tushe ballantana makama, domin kuwa ta kasa gamsar da Kotu, ko kawo hujjojin cewa wanda ake zargin ya aikata laifukan.
"Dadin-dadawa kuma, wanda yake karar, ya kasa tabbatar da kowace hujjar cewa wanda ake tuhuma ya aikata abin da ake tuhumarsa a kai, wanda shi ma zargi maras tushe.
"Sannan rashin kawo wanda dan kasar Kuwaiti, Sheikh Al-Azmi, da hukumar EFCC ta ce, wai Zaura ya damfare shi ko sau daya ne a zaman Kotun, ya nuna zargin na banza ne."
Hakan ta sa Kotun ta wanke A. A. Zaura tun a ranar ranar 9 ga watan Yunin 2020.
A yanzu kuma abubuwan da suke tasowa, a iya cewa, ba sa rasa nasaba da siyasa. Ganin irin gagarunar nasarar da Zaura yake samu yanzu haka a yadda siyasar Kano ke kadawa, a safiyar Laraba, 13 ga Afrikun 2022, Kotun daukaka Kara dake zama a Kano cewa, za a kara dawowa da Shari'ar da aka zartar a shekarar 2020, "Saboda Zaura bai halarci zaman Kotun a lokacin da aka zartar da hukuncin a shekarar 2020 ba."
Aka ce sai dai a koma babbar kotun a sake Shari'ar kuma ba a gaban alkalin da ya yanke wancan Shari'ar ta baya ba.
Tabbas, wannan abu abin mamaki ne kuma abin al'ajabi ne, domin ita kanta dokar da ta ce sai idan wanda ake kara na nan kafin a yanke hukunci, an yi ta ne domin ta kare hakkinsa, gudun kada a yi wani hukuncin da bai yi masa adalci ba.
Don haka wane irin mataki A. A. Zaura ya dauka a yanzu? Jim kadan bayan Kammala wannan Shari'a, Lauyoyin Zaura sun daukaka kara zuwa Kotun Koli, tare da nemo izinin hana wannan Hukunci, har sai Kotun Kolin ta kammala nata shari'ar. Hakan yana nufin, Zaura a yanzu ba shi da wani laifi a idon hukuma.
Kan haka, muke sanar da al'ummar Jihar Kano da 'yan jam'iyyarmu ta APC da dimbin magoya bayanmu cewa a ci gaba daga inda aka tsaya wajen yada manufofin alheri na Mai Girma Abdussalam Abdulkarim Zaura, Kuma munanda yakinin cewa duk Wani tuggu da kulle-kullen 'yan adawar siyasa ba zai yi tasiri ba da yardar Allah.
Muna sane da fadar Allah Madaukakin Sarki a cikin Al'qurani, cewar "Bayan tsanani sai sauki," Aya ta 6 a cikin Sura ta 94. His Excellency Zaura, yana jinjina da godiya bisa nuna damuwa, kwarin gwiwa da adduo'i daga dimbin masoya a ciki da wajen Jihar Kano.
No comments