Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari ya jinjinawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari Masari kan kokarin da gwamnatinsa take yi wajen hidimtawa...
Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari ya jinjinawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari Masari kan kokarin da gwamnatinsa take yi wajen hidimtawa al'ummar Nijeriya.
Masari ya ce Nijeriya ba ta taba samun shugaban kasa kamar Buhari ba tun lokacin da aka kafa kasar a shekarar 1914.
Kalaman na gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, na kunshe cikin wani rahoto da Jaridar, Premium Times ta rawaito, cewa Gwamnan ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mafi nagarta da Nijeriya ta taba samu ta fuskar samar da gwamnati mai inganci.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu, a Katsina yayin wani taron gangami da wadanda suka amfana da shirin tallafi na gwamnatin tarayya wato NSIP a jihar suka shirya,
Masari ya ce, shugaba Buhari ya shimfida ginshiki mai nagarta, kuma idan har gwamnatin gaba ta yi amfani da shi yadda ya kamata, yan Nijeriya da dama za su fita daga kangin talauci.
No comments