Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ƙudirin Osinbajo Na Karɓar Shugabancin Nijeriya, Tare Da Sauya Shugabancin Ƙasar Zuwa Sashin Addini

Rubutu: Farooq Kperogi  Fassara: Ya'u Sule Tariwa  Bari na fara ta hanyar bayanin cewa yawancin mambobin RCCG da na yi hulɗa...


Rubutu: Farooq Kperogi 
Fassara: Ya'u Sule Tariwa 

Bari na fara ta hanyar bayanin cewa yawancin mambobin RCCG da na yi hulɗa tare da su, makonni da suka gabata ba sa tallafawa ko nuna goyon bayansu ga tafiyar Osinbajo.

Da yawa daga cikinsu suna jin kunya bisa ga irin halinsa, kamar yadda ni ma a baya na ji kunya da Buhari ta hanyar nuna soyayya ga musulman arewa tare da yunƙurin basu fifiko.

Saboda haka, kar ayi min mummunan fahimta da cewa ina ƙoƙarin ɓata mambobin RCCG ko ƙungiyar wanda na yi imani cewa babban sashi ne na adddi wanda ya ke da tsarki da tushe.

Yanzu, bari mu fara bayyana ingantattu da tabbatattun hujjoji bisa ga tsattsauran ra'ayin Osinbajo. 

Babbar yaaudarar Osinbajo ya ta'allaka ne ga yawan musulmai da su ke aiki a ofishinsa, wanda ya haɗa da aƙalla biyu waɗanda suka daina aiki a can,  da wasu waɗanda aka naɗa kai tsaye ba tare da sanin Buhari ba ko fadarsa, hakan yunƙurin yin takardun boge ne a kan tsatstsauran riƙonsa na addini da kuma nuna wariya ga ƴan Najeria wanda basu da aƙidar kiristanci musamman ta fannin ibada a cocinsa wato RCCG.

Ga jerin mutane 80 waɗanda suke aiki a ofishinsa, waɗanda yawancinsu, na tabbatar membobin mujami'ar RCCG ne.  Daga cikin mutanen 80 waɗanda suke aiki a ofishinsa, gami da waɗanda suka samu shiga ta hanyar fadar shugaban ƙasa.

Osinbajo shine tsohon malamin majami'a (fasto) na Tree Parish ƙarƙashin RCCG a Legas.

A watan Mayu, na shekarar 2015 loƙacin da ya zama mataimakin shugaba, Okechukwu Enelamah, daga baya yayi nasaran zama fasto a cocin ta Perish. Watanni bayan haka loƙacin da aka ba Osinbanjo damar ƙaddamar da minista, ya zabi Enelamah.

Bayan ɗauko Enelamah a matsayin minista, Alex Ayoola Okoh shine daga baya ya zama sabon fasto na Olive Tree Parish. A shekarar 2017, wata dama ta fito a fannin matsayin DG na BPE wanda Osinbajo ya sake zaɓar Alex Ayola Okoh, magajin Enelemah a karo na biyu.

Waɗannan sune fastoci uku na cocin Olive Tree Parish waɗanda suka yi nasarar shiga cikin gwamnati a loƙaci guda ta hanyar Osinbajo.

Lamarin ya fi bada sha'awa loƙacin da wanda ya riga Osinbajo a Olive Tree Parish fasto Olukayode Pitan, ya ce ya zama fastocin Pioneer na Parish. Ya yi aiki a matsayin babban fasto a can tun daga shekarar 1995 har zuwa 2009 da ya miƙa zuwa Osinbajo.

Haka nan shima Osinbajo ya sanya shi MD Shugaba na Bankin Masana'antu (ba shakka kuma hakan ta tabbata tare da amincewar Buhari wanda ba ya da masaniyar ainihin abin da ke faruwa) loƙacin da yake shugabanci. Wannan fastoci 4 ne na mambobi RCCG Perish.

Joseph Chiedu Ugbo,  MD/CEO na Niger Delta Power Holding Company Limited, shima wani faston RCCG ne؟ kuma Osinbajo ne yayi aiki tuƙuri wajen nema masa muƙamin a loƙacin yana shugaban kwamitin kamfanin؛

Ben Akabueze shima wani shahararren fasto ne na RCCG wanda Osinbajo ya bayarda umarni a naɗa shi a matsayin darektan ofishin kasafin kuɗin tarayya. Ya kasance a baya kuma har yanzu shine fasto na lardin Lagos 39 na RCCG.

Jumoke Oducole, mai ba da shawara na musamman ga Osinbajo a masana'antu, fannin kasuwanci da saka hannun jari (daga 2015-2019) memba ce ta RCCG kuma mijinta Tunde Odule shima malamin majami'a (fasto) ne a cocin ta RCCG.

Afolabi Imoukhuede, wanda ke jagorantar naúrar kirkirar ayyuka na musamman wanda ake kiri (NSIP) a ofishin jingina na ƙasa shima memba ne na Osinbajo, kodayake babu sashihancin kasancewarsa fasto a mujami'ar ta RCCG.

A cikin watan Yuni 20, 2020, yayin hira da Vanguard, yace lokacin da na hadu da shi a 2015, Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi yunkurin ya nada ni a matsayin babban mataimaki na musamman ga Shugaban kasa a kan aikin yi lokacin da ya yi karatu a UNILAG, labarin Vanguard ya zo a ƙarƙashin sashen cocin RCCG.

Edobor Iyamu, daya daga cikin sama da 30 wanda aka nada amma fadar shugaban kasa ta kora a shekara 2019, shima fasto ne a cocin Jesus Family Parish, sashen RCCG dake hanyar Ribadu, Ikoyi a Jihar Legas.

Abu mai ban sha'awa game da alƙawarin shi ne cewa waɗannan Fastocin RCCG koyaushe nuna dabi'un su suke na Kiristanci. Misali, kusan dukkanin ma'aikatan gudanarwa na BOI da fasto Kayode Pitan ke aiki tare da su, su ma mambobin RCCG ne.

Saboda haka, RCCG na Osinbajo ya aiwatar da wani tsari wanda ƙarƙashin kulawar cocin RCCG aka samu ɗaya daga cikin masu kula da mujami'ar wato Enoch Adeboye, ya yi bayani cikin buwaya cewa ɗaya daga cikin membobin cocin ta RCCG ma'ana Osinbajo zai zama shugaban Najeriya.

Yawancin malaman mujami'a ƙarƙashin Pentecostalism dake Najeria kamar su Farfesa Ebenezer Obadare wanda ya rubuta littafi mai suna Pentecostal Republic: Religion and the Struggle for State Power in Nigeria” da kuma Farfesa Ruth Marshall wadda ta rubuta ''Political Spiritualities: The Pentecostal Revolution in Nigeria" sun yi harsashe dangane da wannan natijar.

Tunanin Osinbajo na mulkar Nigeria ta hanyar yin amfani da tsarukan RCCG shine cikakkiyar fahimta ta kan abinda na kira sauya salon tsarin da jamaa suke kai؟

Koƙarin Osinbajo na samun hanyar zama shugaban ƙasa na nuni da cewa manufofinsa shine ya kammala abin da ya fara tun shekarun baya a cocin RCCG dake Lagos.

Zan ci gaba da fallasa ƙudirorinsa a cikin kwanaki ko makonni masu zuwa.

Idan aka zuba idanu, tabbas Osinbajo zai ɗabbaka manufofinsa na tsatstsauran ra'ayi kamar yadda yake gindaye a tsarin cocin RCCG, cikin ƙasar da take da manyan addinai biyu, wanda hakan zai iya haifar da sabuwar tarzoma akan wacce ake fuskanta a Nigeria. 

Ina ta ƙoƙari wajen gargaɗin tare da nusar da Nigeria domin kaucewa shiga masifa, wadda samun shugabancin Osinbajo zai haifar a ƙasar.

No comments