Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Waɗanda Ba Musulmi Ba Sun Taya Musulmai Azumin Ramadan A Saudiyya

  Waɗanda ba Musulmi mazauna Saudiyya sun taya Musulmai yin azumin watan Ramadan da nufin ƙara kusanci da abota tsakaninsu da Musulmai. Sun ...

 


Waɗanda ba Musulmi mazauna Saudiyya sun taya Musulmai yin azumin watan Ramadan da nufin ƙara kusanci da abota tsakaninsu da Musulmai.

Sun ɗauki azumi tare da kiyaye dokokinsa da kuma shan ruwa tare da abokanansu Musulmi a Saudiyya, kamar yadda jaridar Arab News ta wallafa a shafinta na intanet.

Ta ambato ɗaya daga cikinsu yana cewa: “Bai kamata ku yi Ramadan ku ƙadai ba - Wannan lokaci ne na ƙarfafa abokantaka da karimci.”

Wasu daga cikinsu sun ce Azumi ya ƙara masu kusanci da abokansu Musulmi.

A cewar jaridar, duk da cewa akwai bambancin addini, amma ƴan ƙasashen waje waɗanda ba Musulmi na ƙara rungumar al’adun Saudiyya..

Baya ga kasancewar Ramadan watan Ibadah da tasirinsa ga ƙara kusantuwa ga Allah, bincike ya nuna yin azumi na kaucewa ci da sha daga fitowar al fijr zuwa faɗuwar rana yana da fa’ida wajen inganta lafiyar ɗan adam.

No comments