Wakilin ‘yan’uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na Katsina, Shaikh Yakubu Yahaya Katsina ya bayyana goyonsa ga kalaman Shaikh...
Wakilin ‘yan’uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem
Zakzaky na Katsina, Shaikh Yakubu Yahaya Katsina ya bayyana goyonsa ga kalaman
Shaikh Nura Khalid bisa abubuwan da yake faruwa na tabarbarewar tsaro a
Nijeriya. Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi a Markazinsu a yayin
gabatar da Tafsirin Alkur’ani mai Girma na watan Ramadan.
Shehin Malamin ya ce; “Akwai wani Malami da na ji ya
yi magana mai kama da irin wannan ko shekaran jiya Juma’a ne? Wani ko Nura
Khalid ne? Ya yi magana a Masallacin Juma’a waj3n Pre-khudbarsa ya ce; a ki yin
zabe sai an samu zaman lafiya. Abin da ya fada daidai ne kuma ya kamata Malamai
su goyi bayansa ne amma munafukan duk sun yi shiru, karshe an ma tube shi (daga
Limanci) ka ga ashe Malamai na tasiri, kun ga dama na ce maku matsalar tana
wajen Malamai”, inji shi.
Ya ci gaba da cewa; “To duk munafukan sun yi shiru
yanzu ma abin da suke gani laifinsa ne shi ya tsokano wa kansa wanda ya kamata
a goyi bayansa ne kowa ya yi magana ya zama haka take sai ka ga sun sassauko.
Aki yin zaben mana sai mene?” ya tambaya.
Ya kara da cewa; “Saboda haka Malamai su ji tsoron
Allah su gayawa mutane gaskiya wannan Nura Khalid din gaskiya ya fadi kuma ya
kamata a goyi bayansa ko da baka da ra’ayi irin nasa, ko baka cikin kungiyarsa
amma abin da ya fada mafita ce ga al’umma cewa ka da a yi zabe in ba a yi zabe
ba wani abu ne zai faru wanda zai ba mutane dama su samu sauki”.
No comments