An sace wasu mutane da suka hada da dalibai mata na Kwalejin koyar da harkokin kiwon Lafiya ta Zamfara dake Tsafe. Wani malamin kwalejin d...
An sace wasu mutane da suka hada da dalibai mata na Kwalejin koyar da harkokin kiwon Lafiya ta Zamfara dake Tsafe.
Wani malamin kwalejin da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa Jaridar Daily Trust lamarin da safiyar Laraba.
Ya ce masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da daliban ne a dakin kwanansu da ke wajen harabar makarantar.
Ba a dai san adadin daliban da aka yi garkuwa da su ba, amma wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da dalibai biyar.
Lamarin ya zo ne mako guda bayan da aka harbe dan Mamman Tsafe, kwamishinan gwamnatin Gwamna Bello Matawalle a kofar gidan mahaifinsa da ke Tsafe.
No comments