Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Rasuwar Matashi Yana Tsaka Da Limancin Tahajjud Ta Girgiza Al'umma A Zariya

Daga Wakilinmu Wani matashi ya rasu a yayin da yake kan limancin Sallar Tuhajjud a garin Samaru da ke Zariya a Jihar Kaduna. Mar...


Daga Wakilinmu

Wani matashi ya rasu a yayin da yake kan limancin Sallar Tuhajjud a garin Samaru da ke Zariya a Jihar Kaduna.

Marigayin mai suna Mohammed Sani ya rasu ne a daren Lahadin nan da misalin karfe hudu na dare yayin da yake limancin Tahajjudin a Masallacin Layin Alhaji Mai Kifi da ke Samarun Zariya.

Matashin limamin ya riga mu gidan gaskiya ba tare da ya taba yin aure ba kuma jama’a sun shaide shi da rikon gaskiya da amana a tsakanin al’ummar da yake rayuwa da su.

Wannan rasuwar ta girgiza jama’ar yankin Samaru baki daya bisa shekaru da dama ba a shaida rasuwa irin ta Alaramma Muhammad Sani Lawal ba.

Dubban mutane suka yi dafifi wajen halartar sallar gawarsa tare da yi masa kyawawan Fata.

An yi jana’izar matashin da misalin karfe 8:30 na safiyar Lahadin na a garin Samaru Zariya.

No comments