Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa ‘yan bindiga sun afka wa wasu yankunan jihar, inda suka yi awon gaba da dimbin dabbobi tare da harbi...
Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa ‘yan bindiga sun afka wa wasu yankunan jihar, inda suka yi awon gaba da dimbin dabbobi tare da harbi kan mai uwa da wabi.
Majiyoyi daga yakin sun shaida wa shashen Hausa na RFI cewa maharan sun kutsa Kauyukan Kadaddaba da Ruwan Gero na karamar hukumar Anka ta Zamfarar, inda suka tarwatsa al’umma ba tare da samun wani kalubale daga jami’an tsaro ba.
Wata majiya ta ce tun da tsakar ranar jiya Alhamis ne ‘yan bindigar suka fara afka wa mutane, har ma suka shiga kasuwar Ruwan Gero da ke ci, suka yi awon gaba da dimbin shanu da rakuma da sauran dabbobi.
Kokarin kai wa ga rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara don karin bayani a kan wannan lamari ya ci tura.
No comments