'Yan bindiga sun sace wasu Fulani makiyaya ‘yan kungiyar Miyatti Allah guda 10 a jihar Anambra tare da shanunsu 300. Rahotan...
'Yan bindiga sun sace wasu Fulani makiyaya ‘yan kungiyar Miyatti Allah guda 10 a jihar Anambra tare da shanunsu 300.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun bukaci a biya su Naira miliyan 4, a kuma hada musu da bindiga daga iyalan wadanda suka yi garkuwa da su.
Shugaban kungiyar ta Miyetti A na yankin Kudu maso Gabas, Alhaji Gidado Siddiki ya tabbatar da faruwar lamarin.
Siddiki, ya ce lamarin ya faru ne a Unguwar Obene da ke karamar hukumar Ogbaru a Unguwar makiyayan a lokacin da suke barci, da misalin karfe 1:30 na daren wayewar garin yau Asabar.
No comments