‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjoji da dama wadanda suka sace bayan harin da suka kaiwa jirgin kasan da ke kan hanyar zuwa Kadun...
‘Yan bindigar da suka
yi garkuwa da fasinjoji da dama wadanda suka sace bayan harin da suka kaiwa
jirgin kasan da ke kan hanyar zuwa Kaduna daga birnin Abuja a Najeriya, sun yi
barazanar kashe dukkanin mutanen dake tsare a hannunsu idan gwamnatin Najeriya
ta kasa biya musu bukatunsu.
‘Yan bindigar sun yi barazanar ce a cikin wani
faifan bidiyo da suka fitar a ranar Larabar da ta gabata, inda suka ce ba sa
sha’awar a biya su kudi, sai dai gwamnati ta biya musu bukatun da suke nema,
bukatun da ‘yan ta’addan suka yi ikirarin gwamnati ta san su.
Bidiyon, wanda bai kai
minti biyu ba, ya nuna hudu daga cikin ‘yan fashin dajin tare da daya daga
cikin fasinjojin da suka sace Alwan Hassan, wanda Manajan Darakta ne na Bankin
Noma a Najeriya.
Daya daga cikin ‘yan
bindigar da yayi magana da harshen Hausa ya ce an sako Manajan ne a dalilin
tausaya masa saboda shekarunsa da kuma watan Ramadan.
Wani abu da ya dauki
hankali a faifan bidiyon da ‘yan bindigar suka fitar shi ne yadda aka ga daya
daga cikin motoci masu sulken da suka kona a farkon makon nan, yayin fafatawar
da suka da sojojin Najeriya a Birnin Gwari dake Kaduna, abinda ke nufin an nadi
bidiyon ne a sansanin sojoji na Polwire a garin na Birnin Gwari wanda aka kai
wa hari ranar Litinin.
No comments