Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

'Yan Shi'a Sun Bayyana Damuwarsu Kan Ƴan Uwansu 3 Dake Gidan Yari Tsawon Shekaru 9 Da Kama Su

Daga Wakilinmu Harkar Musulunci  ta bayyana damuwarta kan tsare wasu mabiyanta uku a gidan yari na Kuje shekaru tara bayan da hu...


Daga Wakilinmu

Harkar Musulunci  ta bayyana damuwarta kan tsare wasu mabiyanta uku a gidan yari na Kuje shekaru tara bayan da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama su.

Harkar Musuluncin ta bakin Mohammed Abdullahi ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata takardar sanarwa da ya rubuta ya fitar a Abuja.

Abdullahi ya bayyana sunayen wadanda abin ya shafa: Malam Haruna Abbas, Ibrahim Hussain da Adamu Sulaiman.

“Har yanzu waɗannan bayin Allah uku suna tsare kusan shekaru tara ba bisa ka’ida ba, an kama su a wurare daban-daban, a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a jihohin Kano, Kaduna da Legas, inda suka tsare su a asirce ba tare da iyalansu sun san inda suke ba. 

A cewarsa, Malam Haruna Abbas, Ibrahim Hussain da Adamu Sulaiman suna tsare a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a Abuja na kusan shekaru hudu tsakanin watan Fabrairun 2013 zuwa Maris 2017.

“Tsarewar da aka yi musu a hannun DSS ya saɓawa doka domin ba umarnin kotu bane, daga baya an gurfanar da su a gaban kotu, aka mayar da su gidan yarin Kuje bisa umarnin kotu,” inji shi.

Ya ce a lokacin da suka zauna a hukumar ta DSS sun fuskanci gallazawa da cin zarafi wanda ya janyo musu kalubale mai tsanani ga lafiyarsu

“Kafin a kai su gidan yarin Kuje bisa umarnin kotu, ma’aikatar gwamnati ta gurfanar da su a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja 7 a karkashin Mai shari’a Ademola a ranar 06/11/2014,” inji shi.

Abdullahi ya ce daga baya an mika karar zuwa ga mai shari’a Anwuli Chikere a ranar 3 ga Maris, 2017, amma a yanzu haka tana gaban mai shari’a Emeka Nwite bayan Chiikere ya yi ritaya.

Ya ce duk da cewa ana tuhumar su da laifuffukan da suka hada da ta’addanci, cin amanar kasa, aikata laifuka ta yanar gizo da dai sauransu, duk sun musanta zargin da ake musu.

Abdullahi ya ce daya daga cikin wadanda ake tuhumar, Abbas, ya fuskanci tabarbarewar matsalar rashin lafiya.

“Malam Haruna Abbas yana fama da hauhawar jini da wasu cututtuka, wanda rahotanni suka ce ya kara ta’azzara saboda ci gaba da tsare shi a gidan yari. A lokaci guda kuma, an hana shi zuwa ga likitocinsa kai tsaye,” in ji shi.

Ya kuma yi zargin cewa masu gabatar da kara ba su gabatar da isassun shaidun da za su tabbatar da wadanda ake tuhuma da aikata laifin ba.

“Malam Abbas yana da mata da ‘ya’ya goma sha daya (11). Ya rasa ‘ya’ya mata guda biyu yana tsare a gidan yari. Shi ma Malam Hussain yana da mata da ‘ya’ya bakwai (7) sannan Malam Sulaiman yana da mata biyu (2) da ‘ya’ya hudu (4) tare da wasu marayu hudu (4) a karkashin kulawar sa,” inji shi.

No comments