Daga Muhammad Farouk Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, kuma mai neman takarar shugabancin Nijeriya a karkashin jam’iyyar PDP...
Daga Muhammad Farouk
Gwamnan jihar Sakkwato,
Aminu Waziri Tambuwal, kuma mai neman takarar shugabancin Nijeriya a karkashin
jam’iyyar PDP, ya yi tawaye daga matsayar da shugabannin Arewa suka cimma na
tsayar da Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da tsohon shugaban Majalisar
Dattawa ta kasa, Bukola Saraki a matsayin ‘yan takarar shugabancin Nijeriya a
PDP na maslaha daga Arewa.
Tambuwal ya ce matsayar
na shugabannin Arewa ba shi ne yarjejeniyar da suka cimma a zaman da suka yi a
Minna ta jihar Neja ba.
Kungiyar kamfen din
Tambuwal mai suna ‘Tambuwal Campaign Organisation (TCO)’, ta ce labarin ba
gaskiya bane; “hakikanin abin da ya faru shi ne a ranar Larabar 20 ga watan
Afrilun 2022 an hadu a gidan gwamnan Bauchi dake Abuja, inda muka yi duba ga
zaman da aka yi, muka cimma matsaya cewa fitar da dan takarar maslaha ba abu ne
da zai yiwu ba’, kamar yadda Nicholas Msheliza, Daraktan tattara jama’a na
kungiyar TCO ya bayyana.
Idan ba ku manta ba,
Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na
jam'iyyar PDP, shugabannin Arewa a ranar Juma'a 28 ga watan Mayu, sun zabi
tsohon shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki da Gwamnan jihar Bauchi, Bala
Mohammed a matsayin 'yan takararsu.
A cikin wata sanarwa
dauke da sa hannun tsohon mataimakin shugaban jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya,
Farfesa Ango Abdullahi, shugabannin Arewa sun ce an kai ga zaben Saraki da Bala
Mohammed ne bisa wasu sharudda da aka amince da su wajen tantance ‘yan takarar
hudu da suka mika kansu ga tantancewar.
Karanta wannan; Dan Takarar Jam’iyyar PDP Na Maslaha: Shugabannin Arewa Sun Zabi Saraki Da Bala Mohammed
No comments