Mataimakin Gwamnan Kano Nasiru Yusuf ya sauka daga mukaminsa a matsayin Kwamishinan Noma na jihar Kano. Sakon saukar na shi na k...
Mataimakin Gwamnan Kano Nasiru Yusuf ya sauka daga mukaminsa a matsayin Kwamishinan Noma na jihar Kano.
Sakon saukar na shi na kumshe ne a takardar manema labarai da Sakataren watsa labaransa, Hassan Musa Fagge ya sanyawa hannu wanda MADOGARA ta sami kwafi.
A ciki, Gawuna ya mika godiyarsa ga Gwamna Ganduje bisa damar da ya ba shi ya rike mukamin Kwamishinan noma na jihar har na tsawon shekaru bakwai. Wanda ya ce hakan ya sanya ya zama Kwamishinan noma mafi dadewa a ƙasar.
Dr Nasiru Gawuna ya ce ya sauka a mukamin ne domin fadada kudirinsa na siyasa.
Kawo yanzu Kwamishinoni takwas ne suka sauka daga kujerunsu domin shiga takara a zaɓen 2023.
No comments