Ofishin Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fitar da sanarwar ganin jaririn watan Ramadan a fadin Ni...
Ofishin Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fitar da sanarwar ganin jaririn watan Ramadan a fadin Nijeriya.
Ofishin ya wallafa hakan ne a shafinsa na Facebook kamar yadda wakilin Jaridar MADOGARA ya labarto.
Ofishin ya ce; "Mun sami rahotannin ganin jaririn watan Ramadanan na bana 1443".
Ya ci gaba da cewa; "Garuruwan da aka gani yau Juma'ah sun hada da: 1.Birnin Kebbi. Al'ummar gari da yawa sun gani a Unguwar Illelar Yari. 2. Jimeta, Jihar Adamawa. 3. Ringim, Jihar Jigawa. 4. Unguwar Inwala, Damagaram, Jumhuriyar Nijar", ya labarto.
Ya kara da cewa; "Har yanzu ana samun karin rahotanni. Don haka gobe Asabat zai zama 1 ga Ramadan 1443, in sha Allah", suka jaddada.
No comments