Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kasuwar 'Yantumaki Dake Jihar Katsina

Labarin dake shigowa Jaridar MADOGARA a halin yanzu na nuni da cewa; wadansu 'yan bindiga sun farmaki kasuwar 'Yantumak...


Labarin dake shigowa Jaridar MADOGARA a halin yanzu na nuni da cewa; wadansu 'yan bindiga sun farmaki kasuwar 'Yantumaki dake karamar Hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

Majiyarmu ta labarta mana cewa; 'yan bindigar sun afkawa kasuwar ne ana tsaka da cin kasuwar da misalin karfe 3 na yammacin yau Juma'a. 

Ya zuwa haɗa rahotan nan 'yan bindigar sun kashe mutane da ba a tantance ba, amma ta labarta mana cewa; ta ga gawarwakin mutum uku da aka tafi da su asibiti. 

 Har wala yau 'yan bindigar sun barnata dukiyoyin al'umma na miliyoyin nairori tare da raunata mutane da dama da kuma garkuwa da adadin da ba a kai ga tantancewa ba ya zuwa haɗa rahotan nan. 

No comments