Daga Wakilinmu Wata haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Matasan Jihar Bauchi mai suna 'Bauchi For Change Group' sun sha alwashi tare da ...
Daga Wakilinmu
Wata haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Matasan Jihar Bauchi mai suna 'Bauchi For Change Group' sun sha alwashi tare da rantsuwar zasu maka Dr. Nura Manu Soro a kotu matuƙar bai fito takarar Gwamnan jihar ba a wannan zaɓen mai zuwa.
Ƙungiyar ta bakin shugabanta Comrade Yahaya M Abdullahi sun fitar da sanarwar ne ga manema labarai a daren Juma'a, inda suka bayyana takaicinsu ganin yanda halin da dubban ƴan Uwansu Matasa ke ciki, kana kuma suka yi alƙawarin zasu tsaya da dukkan ƙarfinsu don ganin Dr. Nura ya zama Gwamna a Jihar ta Bauchi.
“Mune Matasa a wannan Jihar, mu muka san abunda ke gudana, mune muke zagaya wa tare da karaɗa dukkan faɗin jiharmu, musamman cikin ƙwaryar garin Bauchi, muna da matasa sama da Mutum dubu a zaune waɗanda basu komai, ba sana'ar yi, wasu daga cikinsu sun yi karatu babu aikin yi, wasunsu na zaune, mungode Allah kwanakin baya Dr. Nura yayi ta raba ma wasu guraben karatu kyauta shima yana daga cikin abunda ya rage mana wani raɗaɗin.”
Gwamnatoci da dama sunzo kuma sun shuɗe kowa yayi bakin ƙoƙarinsa a irin ɓangaren daya ɗauka, to mu muna bukatar Ɗan uwanmu Matashi ne a yanzu domin shine yasan ciwon mu da kuma abunda ke damunmu, saboda haka muna kira gare shi daya taimaka mana a wannan Jihar ya fito neman takarar Gwamna, mu kuma sai inda ƙarfinmu ya ƙare, zaku mara masa baya Ɗari bisa ɗari har nasara.” Inji Shugaban tafiyar Comrade Yahaya M Abdullahi.
Ya ƙara da cewar “Matuƙar Dr. Nura Manu bai fito takarar Gwamna a Bauchi ba a wannan halin da muke ciki, lallai mu matasa zamu maka shi a Kotu, sannan kuma zamu bayyana shi a matsayin wanda bai mana adalci ba a wannan halin da muke ciki na rashin abubuwa da daman gaske.”
No comments