Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zaɓen Faransa: Da baƙiƙƙirin gara baƙi-baƙi - Daga Muhsin Ibrahim

  Za a yi zaɓe zagaye na biyu a ƙasar Faransa ranar Lahadi mai zuwa. Duba ga yadda shugaba mai ci, wato Emmanuel Macron, ya yi ƙaurin suna a...

 



Za a yi zaɓe zagaye na biyu a ƙasar Faransa ranar Lahadi mai zuwa. Duba ga yadda shugaba mai ci, wato Emmanuel Macron, ya yi ƙaurin suna a ƙasar Hausa (tsakanin Musulmai), mutane da dama suna fatan ya faɗi. Mutane ba su san cewa gara shi da matar da yake takara da ita ba sau 100.

Marine Le Pen, a takaice, ƴar siyasa ce mai tsaurin ra'ayi. Tana da ƙyamar baƙi da Musulmai da kuma musulunci. Ta yi alƙawarin hana saka hijabi (mayafi da ɗan kwali) muddin ta ci zaɓen nan. Duk da alƙaluma sun nuna Macron yana gaban ta, ana zaton za ta iya ci.

A muhawarar da ƴan takarar suka yi jiya, Macron ya faɗa mata cewar hana Musulmai saka hijabi a ƙasar Faransa zai iya haddasa yaƙin basasa (wato "civil war"). Musulmai sun kusa kaso goma (10%) na mutanen Faransa. Wato adadin su ya kusa miliyan shida. 

Na yi wannan gajerin rubutun ne don wayar da kan ƴan uwa da suke tsinewa Macron suke fatan Le Pen ta yi nasara a bisa rashin sani. Ai da baƙiƙƙirin, gara baƙi-baƙi.

Allāh dai ya zaɓa musu/mana mafi alheri, amin.


No comments