Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Zanga-zangar Kungiyar NLC A Zamfara, Majalisar Dokoki Ta Shiga Tsakani

Daga Hussaini Yero, Gusau Masu iya magana na cewa, rana bata karya sai dai uwar diya ta ji kunya, yau saura mako guda ke nan wa&...


Daga Hussaini Yero, Gusau

Masu iya magana na cewa, rana bata karya sai dai uwar diya ta ji kunya, yau saura mako guda ke nan wa'adin da Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta dauka karkashin shugaban Majalisar Honorabul Muazu Magarya na sasanta Kungiyar Kwadago watau NLC reshen Jihar Zamfara, Karkashin Jagorancin Kwamared Sani Haliru da gwamnatin jihar Zamfara, karkashin Jagorancin Gwamna Bello Matawallen Maradun.

Majalisar Dokokin jihar Zamfara, ta shiga sulhu ne tsakaninta da Kungiyar Kwadago sakamakon shirya gagarumin zanga-zanga don bayyanawa duniya halin da ma'aikatan jihar ke ciki na mawuyacin hali da kin ba su hakokinsu da gwamnatin duk da matakan sulhu da tattaunawa da jami'an gwamnatin da kungiyar Kwadago ta sha yi wanda babu adadi amma gwamnatin ta yi watsi da su kai ka ce ba sune zuciyar gwamnatin jihar ba. 

Zaman sulhun da kungiyar Kwadago da yarjejeniyar dage zanga-zangar na dauke ne a takardar da ma'taimakin Kilak, Muhammad Aliyu ya sanya ma hannu a ranar 30/03/2022, wacce Majalisar Dokokin ta aikawa shugaban Kungiyar Kwadago kwamared Sani Halliru.

A binciken da wakilinmu ya yi kan batun zanga-zangar, lallai shugabannin  Ma'aikatan jihar Zamfara, na kownane bangare sun shirya tsaf akan batun zanga-zangar ko a mutu ko a yi rai sakamakon watsi da hakkokin ma'aikatan da doka ta ce a ba su ba alfarma ba musamman ma ma'aikatan kananan hukumomi da har yanzu akwai masu amsar karancin albashi na dubu shida ba ma na dubu sha takwas ba ko talatin.

Haka su ma tsoffin Ma'aikatan 'yan fensho suma suna cikin tsaka mai wuya wajen biyan kudin fensho wata-wata ana samun tsaiko bama batun kudin sallamar su na aiki ba.

No comments