Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Al’ummar Yankin AMAC/Bwari Sun Amince Candido Ya Fito Takarar Majalisar Wakilai

Daga Bello Hamza, Abuja Bayanai sun nuna cewa, masu fada aji a bangarori da daban-daban na yankin mazabar majalisar wakilai ta t...Daga Bello Hamza, Abuja

Bayanai sun nuna cewa, masu fada aji a bangarori da daban-daban na yankin mazabar majalisar wakilai ta tarayya ta AMAC/Bwari na yankin babban birnin tayayya Abuja sun amince tare da kira ga shugaban karamar hukumar AMAC, Hon. (Dr) Abdullahi Adamu Candido, ya fito don wakiltarsu a majalisar tarayya Abuja a shekarar 2032.

Wannan bayani na kunshe ne a takardar sanarwar da jami’in watsa labaransa Chif Dayo Lawal, ya sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai a Abuja.

Sanarwa ta kuma kara da cewa, “A halin yanzu Shugaban karamar hukumar AMAC Hon. (Dr) Abdullahi Adamu Candido, ya amince da karaye-kirayen al’ummar yankin AMAC/Bwari na neman ya wakilcesu a majalisar wakilai, ya amince da kiraye-kirayen da mata, matasa da dukkan masu fada a ji a daga mazabu 22 na yankin suka yi, kuma tabbas ba zai basu kuya ba.

“Masu wannan kiran sun dogara ne da irin ayyukan alhairi na raya kasa da Candido ya gudanar a zamansa na shugaban karamar hukumar AMAC, suna kuma fatan wannan matsayi da zai kai, zai kara masa kaimi wajen yi wa al’umma ayyukan bunkasa rayuwarsu’’

Idan za a iya tunawa, Candido ya so ya jingine harkar siyasa bayan ya gama wa’adinsa na shugabancin karamar hukumar AMAC amma kuma ba zai iya watsi da wannan kira na al’umma ba.

Fatanmu a nan shi ne Allah ya taimaka masa, don kuwa mutum ne mai sa al’amurran al’umma a gaba” in ji wani mazaunin unguwar Jabi.

No comments