Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Kai Harin Ta'addanci Fiye Da Dubu 5 Cikin Shekaru 3 A Yammacin Afrika

  Manyan hafsoshin tsaron kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS sun fara taron kwanaki 2 a kasar Ghana domin nazari akan matsalolin tsaron da...

 


Manyan hafsoshin tsaron kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS sun fara taron kwanaki 2 a kasar Ghana domin nazari akan matsalolin tsaron da suka addabi yankin da kuma yadda za su hada kai domin tinkarar su.

Nijeriya da Nijar da Mali da Burkina Faso na daga cikin kasashe 15 dake cikin kungiyar dake fama da matsalar tsaron dake da nasaba da ayyukan ta’addanci, yayin da kasashen Ghana da Jamhuriyar Benin da Cote d’Ivoire ke fargabar fantsamar tashin hankalin zuwa kasashensu.

Ministan tsaron Ghana Dominic Nitiwul ya bayyana cewar matsalar tsaro daga kungiyoyin dake dauke da makamai da masu aikata manyan laifuffuka na karuwa a yankin.

Nitiwul ya bukaci musayar labaran asiri a tsakanin jami’an tsaron domin tinkarar ayyukan wadannan batagari wadanda ke jefa rayuwar jama’a cikin hadari.

Ministan ya ce a matsayin su na kwararu ya dace su yi watsi da batun maganar al’ada da addini da kasa wajen hada kai a tsakanin su da zimmar samun nasara.

Nitiwul ya ce a cikin shekaru 3 da suka gabata, yankin ya fuskanci sama da hare-haren ta’addanci 5,300 abin da ya yi sanadiyyar hallaka mutane kusan 16,000, yayin da a cikin watanni 3 na wannan shekarar aka samu hare-hare sama da 840.

No comments