Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Samu Rikici A Unguwar Deidei Abuja

©BBC Rundunar ƴan sandan Najeriya na kokarin kwantar da wata tarzoma da ta barke a unguwar Dei-Dei a kasuwar kayan gini a Abuja....


©BBC

Rundunar ƴan sandan Najeriya na kokarin kwantar da wata tarzoma da ta barke a unguwar Dei-Dei a kasuwar kayan gini a Abuja.

Kawo yanzu mutum guda ne aka tabbatar da mutuwarsa sanadiyar rikicin tare da jikkatar wasu da dama.

Wani mazauni yankin ya shaida wa BBC cewa tarzomar ta samo asali ne bayan da wata babbar mota ta take wata mata da ke kan acaba, lamarin da ya sa aka kone babur din, wanda kuma ya fusata ƴan acaba suka shiga kone shaguna da farfasa ababen hawa.

Rahotanni sun ce rikicin na neman rikidewa zuwa na kabilanci tsakanin Hausa da ƴan kabilar Igbo.

No comments