Daga Wakilinmu Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya bayyana cewa ana yakar mutanen Nijeriya amma sam ba su gane hakan ba. Wakilinmu ya labarto ma...
Daga Wakilinmu
Shaikh Ibraheem
Zakzaky, ya bayyana cewa ana yakar mutanen Nijeriya amma sam ba su gane hakan
ba. Wakilinmu ya labarto mana cewa; Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a yayin
ganawarsa da wadansu ba’adin almajiransa a gidansa dake Abuja a ranar Juma’a 6
ga watan Mayun 2022.
Shehin Malamin ya ce; “Wannan
irin ƙasa, mutane suna ta ɓaganniya, ana yaƙarku amma ba ku gane ba. (Ana kaɗa
ku) kamar shanu. Ka san saniya ina ruwanta in ma ƙwata za a kai ta (a yanka)?
Ana tafiya tana cin ciyawarta.... Amma mutum wanda yake da hankali, kuna gani
ana neman a ƙarisa ku, a gurgunta ku da ƙarfin tsiya.
Ya ci gaba da cewa; "Har
ma an riga an gama gurguntawar, ana ta ta yi ne, kudinku baya sayan komai. A
1980 Dala 1 ne Naira 2, Yanzu Naira 570+ ne Dala 1, amma da kuwa Naira 2 ne
Dala 1. To kuma amma wai mu ke da 'Golden Zone', amma kudinmu bai da daraja. Mu
nan irin diban 'Gold' din da suke a kewayen Zamfara din nan, Helicopters suke
zuwa da shi su yi ta diba, har mutane sai su ce sun ji karar jirgin sama, wasu
Helikwaftoci ne, kuma 'Gold' ake diba a yi waje da su, ba tare da biyan ko
kwabo ba. Kuma su wadanda ake cewa shugabannin sun sani. Su abin da ya dame su
kawai a ba su nasu kason”, ya tabbatar.
A wani bangare na
bayaninsa, Shehin Malamin ya ce; "Kuma ni na lura magana ma in ka yi ma
(kamar) ba amfani, saboda su mutanen kasar nan ma in ka yi maganar ma suna cewa
kai mahaukaci ne. Wata rana da nake magana din nan, su wadanda nake maganar don
su lura amma ba su damu ba, amma sai aka ce har wani Janaral ya daki tebur, ya ce
wannan mutumin 'is dangerous!' ka ga yana magana da Talakawa ne. Lokacin da
nake cewa ku gane ba wata Boko Haram, mai suke diba, yanzu haka akwai rijiyar
mai 25 a Borno, mai ake diba. Shi ne ya bugi Tebur yana cewa akwai hadari don
ana fadawa talakawa ne. To su kuma talakawar ba su damu ba ma,”, inji shi.
"Wato muna wata
irin kasa ce da komai ya faru, in musiba ta samu wani mutum, sai ka ga kamar ma
har murna suke yi. Sai su yi ta murna. Ka san da ban mamaki ko? Idan musiba ta
samu wani sai ka ga wani yana murna. Shima sai tasa ta zo, sai ya yi bakin
ciki, sai wani kuma shima ya masa murna. Sai ta je ga wancan, ka ga ba wanda ya
san yaushe za ta kare ke nan”, ya lurantar.
"Yanzu wa ya san
ya al'amari zai kasance nan da baÉ—i, ko kuma bayan shekara biyu zuwa uku? Tunda
abubuwan suna gudu ne ba kadan ba, gudu suke ba kadan ba. Da ana bin jirgin
kasa, an fi aminci, to yanzu jirgin kasan ka ga abin da suka yi masa. To daga
nan kuma ka ga yanzu ba aminci ke nan a jirgin ma ko da an gyara shi.... Su
abin da kowanne (daga Mahukuntan Kasar nan) yake da bukata shi ne a bashi
mukami, ala bashi a yi duk abin da aka ga dama. Ko me aka ga dama a yi, shi dai
a bashi mukami. To. Idan ka ce ga mafita, mutane suka ce ba haka nan bane. Ya
za ka yi da su? Ba sai ka kyale su ba? Mu ce to shi ke nan ku nemi mafita inda
za ku samu. Amma an ce musu ga mafitar, sun ce ba haka bane”.
Shaikh Zakzaky da yake
magana dangane da mafitar kasarnan ya labarta cewa; "wasu su kan ce eh
gaskiyarka ne, musulunci din ne mafita, amma fa kai kana nufin Shi'a ne, mu
kuma ba za mu yi Shi'a ba. Ta wani dan Tawayiyya ya ce, wai yanzu in ma aka yi
'revolution' a kasar nan za a kafa Gwamnatin Shi'a ne, shi kuma da a yi Shi’a
gara ma a ci gaba da Dimokuradiyyar. Ya ce gara 'Status quo' da ISLAM wanda shi
a wajensa sunansa Shi'a. To sai mu ce ai ba wata matsala, kai ka yi Sunnah
Islam din mana. Shi kuma ba zai yi ba. Sunnah Islam din nasa shi ne ya bi
azzalumai. Ya samu nasa kason.
"To yanzu kuma na
ga ko a Shi'a din ma abin da (wasu) suke ta matsawa a kan mu ke nan. Wai sai mu
hada kai da azzalumai mu rayu. Shi kuma azzalumi ba ruwansa shi, ko me ka masa,
ko Sujjada ka masa ma yanka ka zai yi. Ko Sujjada ka masa, ka ce yanzu ka tuba
ka maishe shi Ubangiji, zai ce kai Sujada mu gani. In ka yi ya dauko bindiga
(ya nemi ya kashe ka). Duk abin da ka masa ba zai ta a yarda da kai ba (matukar
ka taba masa bara'a). Amma ta yiwu in tun farko dama baka masa tawaye ba, kana
tare da shi ne, ya zama ka samu rabonka a wajensa.....", inji shi.
No comments