Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

APC Ta Ƙara Wa'adi Yayin Da 'Yan Takara Ke Tururuwar Sayen Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa

  Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ƙara wa'adin sayar da fom ɗin takararta a dukkan matakai yayin da 'yan takara ke ƙara tu...

 


Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ƙara wa'adin sayar da fom ɗin takararta a dukkan matakai yayin da 'yan takara ke ƙara tururuwar sayen tikitin takarar shugaban ƙasa.

Tun farko an tsara kammala sayar da fama-faman ne a ranar Juma'a, 6 ga watan Mayu.

Sai dai, cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran APC na ƙasa ya fitar ranar Laraba, jam'iyyar ta ƙara wa'adin zuwa ranar Talata, 10 ga Mayu.

A cewar wani sabon jadawali da Sakataren Tsare-Tsare na APC na Ƙasa Sulaiman Muhammad Argungu ya fitar, an saka ranar 11 ga Mayu a matsayin ranar da dukkan 'yan takara za su miƙa fama-faman da suka cike.

Yanzu za a gudanar da tarukan zaɓar wakilai wato daliget a dukkan ƙananan hukumomi na Najeriya daga 12 zuwa 14 ga watan na Mayu.

Lamarin na zuwa ne yayin da jam'iyyar ke ci gaba da samun 'yan takara musamman na shugaban ƙasa, inda a jiya Laraba Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi da tsohon shugaban jam'iyyar Adams Oshiomole suka ƙaddamar da takarar tasu.

Kazalika, ana sa ran Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar zai ayyana tasa takarar a APC.

No comments