Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Atiku Abubakar Ya Lashe Zaɓen Fitar Da Gwani Na PDP

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya lashe zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PD...


Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya lashe zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP.

Atiku ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri'a 371. Ya kayar da gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike wanda ya zo na biyu da ƙuri'a 237.

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, kuma shugaban kwamitin ya gudanar da zaben, David Mark, ne ya bayyana sakamakon zaben wanda aka gudanar a Abuja, babban birnin kasar.

A jawabin da ya yi bayan nasarar da ya samu, tsohon mataimakin shugaban kasar ya caccaki gwamnatin APC mai mulkin Najeriya, yana cewa ta ja wa kasar koma-baya, kasancewar babu abin ta yi sai warwarare ayyukan alherin da ya ce jam`iyyarsa ta PDP ta shuka gabannin APC ta yi mata kaye a shekara ta 2015.

Ƙuri'ar da kowanne ɗan takara ya samu

Tariela Oliver 1
Sam Ohabunwa 1
Pius Anyim 14
Udom Emmanuel 38
Bala Mohammed 20
Bukola Saraki 70
Nyesom Wike 237
Atiku Abubakar 371
Ayo Fayose 0
Dele Momodu O
Charles Ugwu 0
Chukwendu Kalu 0

Ba wannan ne farau ba

A shekarar 2019 ma Atiku ya yi wa PDP takara, amma ya yi rashin nasara a babban zaɓe, wanda Shugaba Muhammadu Buhari mai ci ya lashe.

Atiku, mai shekara shekaru 75, zai fuskanci duk wanda APC za ta tsayar a nata zaɓen da za ta yi a ranakun shida da bakwai na watan Yuni.

Wannan ne karo na uku da aka zabi Atiku Abubakar don yin takarar shugaban ƙasar Najeriya ba tare da ya samun nasara ba.

No comments