Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ba A Kona Gidana Ba - Bishop Kukah Ya Karyata Jita-jitar Kona Gidansa A Sakkwato

Bishop Matthew Hassan Kukah ya karyata jita-jitar da ta dinga yawo a shafukan sada zumunta da take cewa an kona gidansa da yake ...Bishop Matthew Hassan Kukah ya karyata jita-jitar da ta dinga yawo a shafukan sada zumunta da take cewa an kona gidansa da yake Sokoto hade da kudi wajen Naira biliyan daya a wani daki. 

Masu amfani da shafukan sada zumunta musamman 'yan kungiyar yan aware ta IPOB su ne suka dinga cewa an kona gidan nasa domin su bayyana yadda zanga-zanga a Sakkwato ta koma tashin hankali. 

A hirarsa da gidan jaridar The Cable ta wayar tarho a ranar Asabar, Kukah ya bayyana cewa labarin da ake yadawa karya ne domin gidansa na nan lafiya kuma ba abin da ya sameshi. 

Tun bayan kashe Deborah Samuel bayan an yi zarginta da batanci ga Annabi Muhammadu (SAW), Kukah ya yi ta kokarin a sulhunta tsakanin Kirista da Musulmi a Nijeriya inda a bayaninsa yake cewa addinan biyu sun zauna lafiya da juna tsawon shekaru a garin Sakkwato.

No comments